Talakawan Najeriya na shanawa da Naira Dubu N5,000 har su yi asusu, inji Sadiya Farouk

Talakawan Najeriya na shanawa da Naira Dubu N5,000 har su yi asusu, inji Sadiya Farouk

  • Ministan ayyukan jin kai da walwala, Sadiya Umar Farouk, ta ce tallafin N5,000 da gwamnati ke rabawa talakawa yana taimaka musu
  • Ministan ta ce wasu idan suka karɓi kuɗin har kuka suke su zubda hawaye saboda talauci, kuma tana canza musu rayuwa
  • Duk wanda kaji ya kushe shirin to yana da karfi ne, amma ba karamin jin daɗi yan Najeriya ke yi ba, inji Sadiya

Abuja - Ministan ayyukan jin kai da walwalar al'aumma, Sadiya Umar Farouk, ta ce dama ce ke sa wasu ke ganin Naira Dubu N50,000 da FG ke baiwa masu ƙaramin karfi ta yi kaɗan.

The Cable ta tattaro cewa Ministan ta yi wannan furucin ne yayin da take zantawa da yan jaridan fadar gwamnatin tarayya a Abuja.

Sadiya Farouk ta faɗi wannan kalaman ne yayin da aka mata tambayar ina aka kwana a shirin gwamnatin Buhari na ceto yan Nejriya N100 miliyan daga ƙangin talauci.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

Ministar harkokin jin kai da walwala, Sadiya Farouk
Talakawan Najeriya na shanawa da Naira Dubu N5,000 har su yi asusu, inji Sadiya Farouk Hoto: @Sadiya_farouq
Asali: Twitter

Ministan ta kuma ƙara da cewa shirin tallafin ba zai ɗauki cikin ajin wasu yan Najeriya ba, amma yana taka rawar gani a rayuwar talakawan Najeriya.

A jawabinta, Sadiya Farouk ta ce:

"Idan ka duba irin mutanen dake karban wannan Tallafin, N5,000 na da matuƙar muhimmanci a wurin su saboda talakawa ne da magidanta masu karamin karfi, kuma yana canza rayuwar su."
"Amma kamar ni da kai (ɗan jarida), Dubu N5,000 ba za su isa mu sayi katin waya ba, wannan shi ne banbancin."
"Amma ga waɗan nan mutanen a ƙauyukan su, kuna gani da idanun ku, har asusu suke yi daga cikin N5000 ɗin da ake ba su.

Ko amfanin me tallafi kewa masu cin gajiyarsa?

A cewar Sadiya Farouk, wasu idan aka damƙa musu N5,000 kuka suke na uban gari, suna zubar da hawaye, saboda ba su taɓa rike kamar su ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da mata, da 'ya'yan babban jami'in gwamnatin Matawalle a Zamfara

"Idan ka ji mutane na cewa N5,000 ba zata rike mutum ba, dama suka samu maganar gaskiya, mun fita, mun ga yadda wasu ke kuka da hawaye idan suka karbi kuɗin, ba su taba rike N5,000 ba."
"Dan haka tana jima wa a wurin su, ta canza musu rayuwa, saboda haka mun tsamo su daga wani mataki zuwa na sama da shi."

A wani labarain na daban kuma Gwamna Yahaya Bello ya roki shugabannin APC du nuna masa goyon baya ya samu nasarar gaje Buhari a 2023

Bello, ɗaya daga cikin waɗan da suka ayyana takarar kujerar shugaban ƙasa, yace ya kamata gida su fara nuna masa tsantsar goyon baya.

Ya ce matukar mutane suka tasa abu a gaba da yakini, da izinin Allah za su ci nasarar wannan abun cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel