Ni ba zan kore ku ba: Gwamna Zulum ya gano Malamai 3800 ba su da abinci a koyarwa

Ni ba zan kore ku ba: Gwamna Zulum ya gano Malamai 3800 ba su da abinci a koyarwa

  • An kafa wani kwamiti domin ya yi bincike a kan malaman makarantu na matakin karshe a Borno
  • Jarrabawar da kwamitin ta gudanar ya nuna cewa 31% na malamai 17, 000 ba su san kan aiki ba
  • Gwamnan jihar Borno ya yi alkawari ba zai kori malamai 3,800 da aka samu ba za su iya aikin ba

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum ya bukaci kwamitin da ya kafa ya gudanar da gwaji a kan malamai 17, 299 da ke kananan hukumomi 27 a Borno.

A ranar Alhamis, 17 ga watan Fubrairu 2022 ne Kwamishinan harkar ilmi na jihar Borno, Lawan Wakilbe ya gabatarwa gwamna da rahoton binciken na su.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana shafinsa na Twitter da kuma Facebook, Lawan Wakilbe ya ce an gudanar da gwajin ne a watan Junairu domin ayi gyara.

Kara karanta wannan

N-Power: Gwamnatin Tarayya za ta gwangwaje matasa 300, 000 da kudin jari inji Minista

Sakamakon binciken ya nuna a malamai 17,229 da ake da su, 5,439 (31.6%) ne kawai suka dace su koyar, yayin da malamai 3, 815 ba su cancanci koyarwa ba.

An gano cewa babu wani horo da wadannan malamai fiye da 3, 800 (22.1%) za su iya dauka. Akwai kuma wasu 2,389 (13.9%) da suke aiki ba tare da takardu ba.

Inda abin ya yi kamari

Za a ga cewa a yankin Abadam da ake da malamai 224, 14 rak ne suka dace da koyarwa, 74 sai sun samu karin horo, 136 kuwa ba za su iya daukar horo ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Zulum
Gwamnan Borno da Kwamishinan ilmi Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Rahoton ya ce idan aka bi diddiki, haka abin yake a Kala-Balge inda malamai 21 suka ci wannan jarabawa, 133 su na neman horo, 118 ba su da abinci a malanta.

An fi samun malaman da ba su cancanta su rika koyar da yara ba a Maiduguri. Alkaluman ya nuna Askira-Uba, Chibok, Biu da Bama ne suka biyo bayansu.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Takardun malaman Borno

Sakamakon binciken ya nuna 9.8% na malaman Borno ne kawai suke da digiri, kimanin 8, 100. 47% su na da NCE, yayin da 4.1% suke aiki da shaidar Grade II.

Malamai 2, 281 da ake da su a jihar Borno su na aiki ne da shaidar SSCE/GCE, ragowar 2, 389 da suka rage kuma su na aiki ba tare da su na da shaidar karatu ba.

Martanin Gwamnati

Mai girma Babagana Zulum ya yaba da aikin wannan kwamiti, ya ce dole a gyara harkar ilmi. Zulum ya ce ba zai kori malaman da ba za su iya aikin koyarwa ba.

Gwamnan ya ce zai maida su zuwa wasu wuraren dabam su yi aiki kamar yadda aka bada shawara. Za a iya tura su ma’aikatun muhalli domin su shuka itace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel