Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai hari sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia inda suka kashe mutane da dama
  • Harin wanda aka kai a tsakar daren ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, ya sanya al'umman yankin cikin firgici
  • Zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun karbe wajen domin tabbatar da zaman lafiya

Abia - 'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a yayin wani farmaki da suka kai sabuwar kasuwar shanu ta Abia da ke Omumauzor, karamar hukumar Ukwa West da ke jihar Abia.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa maharan sun kai farmakin ne a daren ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu.

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama
'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An tattaro cewa harin tsakar daren ya sanya mazauna kauyen cikin halin firgici da tsoro.

Rahoton ya kuma kawo cewa jami’an tsaro sun karbe yankin domin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga sun bindige yan sanda uku har lahira a Ofis

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan Bindiga sun bindige yan sanda uku har lahira a Ofis

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa wasu miyagun yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda uku a jihar Ebonyi, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida mana cewa yan ta'addan sun bindige yan sandan har Lahira ne da daren ranar Litinin a gaban Caji Ofis dake kan babbar hanyar Enugu-Abakaliki.

Yan sandan, waɗan da aka rahoto sun saka shinge a kan hanya, sun rasa rayuwarsu ne yayin da yan bindigan suka farmake su, kuma suka buɗe musu wuta.

Majiyar ta ƙara da cewa yan bindiga sun zo ne a cikin babbar Motar Bas, wanda yan sandan suka yi tsammanin motar yan kasuwa ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng