Wata sabuwa: Daraktan FHA na iya fuskantar kora bisa zargin rashin da'a

Wata sabuwa: Daraktan FHA na iya fuskantar kora bisa zargin rashin da'a

  • Kwamitin ladabtarwa na hukumar kula da gidaje ta tarayya (FHA) ya nemi Abdulmumin Jibrin wanda ya kasance darakta a hukumar da ya gurfana a gabansa
  • Ana dai zargin tsohon dan majalisar na Kano da aikata rashin da'a a yayin gudanar da aikinsa
  • Jibrin na iya fuskantar kora idan har ya gaza kare kansa yadda ya kamata a gaban kwamitin

Kwamitin ladabtarwa na hukumar kula da gidaje ta tarayya (FHA) ya aika sammaci ga Abdulmumin Jibrin wanda ya kasance daraktan hukumar kan zargin rashin da’a.

Dalilin kwamitin na gayyatar Jibrin

A cikin wata wasika mai kwanan wata 15 ga Fabrairu zuwa ga Jibrin, shugaban kwanitin, Zubairu Salihu, ya ce an sammaci tsohon dan majalisar na Kano ne saboda ya ki amsa tambayar da aka aike masa da farko.

Kara karanta wannan

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

Wata sabuwa: Daraktan FHA na iya fuskantar kora bisa zargin rashin da'a
Wata sabuwa: Daraktan FHA na iya fuskantar kora bisa zargin rashin da'a Hoto: PM News
Asali: Depositphotos

An nada Jibrin a matsayin daraktan ci gaban kasuwanci na hukumar FHA a watan Agustan 2020. Nadin ya biyo bayan tsige shi da kotu ta yi a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya.

A cikin wasikar da aka gano a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu, Salihu ya ce ana sa ran tsohon dan majalisar ya gurfana a gaban kwamitinsa a ranar Juma’a a ofishin FHA da ke Abuja, The Cable ta rahoto.

Salihu ya ce aikin kwamitin ba zai wofanta ba idan tsohon dan majalisar ya ki zuwa ya kare kansa a kan zargin da ake masa.

Ba a bayyana rashin da’ar da ake magana a kai ba a cikin wasikar amma dai Jibrin na ta yiwa Bola Tinubu, mai neman takarar shugaban kasa kamfen wanda hakan ya sabawa ka’idar aikin gwamnati.

Kara karanta wannan

Wata miyar: Kasa a Afrika za ta fara biyan 'yan zaman kashe wando albashi N41k

Solacebase ta nakalto wasikar tana cewa:

“Dan Allah ka tuna tuhumar da manajan darakta ya yi maka kan zargin nuna gagarumin rashin da’a a yayin gudanar da aikinka, da kuma kin amsa tuhumar kamar yadda aka bukata a tsarin aikin gwamnati.
“Sakamakon haka hukumar a zamanta na al’ada na uku da aka gudanar a ranar Talata, 2 ga watan Fabrairun 2022 ta kafa wani kwamitin bincike da ladabtarwa domin ya binciki dukkan manyan zarge-zargen da aka yi maka.
“A wannan rana, za a gabatar da tambayar matakin da za a dauka a kanka da ya hada da tsigewa ko kora (idan akwai bukatar hakan) sannan ana bukatar ka gurfana a gaban kwamitin don kare kanka da kanka.
“Kana kuma da hurumin kawo shaidu, idan bukatar hakan ya taso. Dan Allah ka sani cewa rashin bayyanarka ba zai wofantar da tsare-tsaren kwamitin ba.
“Wannan gayyata an yi shi ne daidai da layi 8.2.0 na tsarin aiki na hukumar gidaje ta tarayya, 2008 da kuma sashi 030307 na tsarin aikin gwamnati (2009)."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP

Cin amanar aiki: An daure jami'in gwamnati bisa ba kwangilar bogi a jihar Bauchi

A wani labari na daban, mai shari’a Muazu Abubakar na babbar kotun jihar Bauchi, ya zartar da hukunci a kan wani Baba Suleiman Darazo, babban direba a hukumar shari’a ta jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar AUPCTRE reshen Bauchi.

A ranar Talata ne Alkali Abubakar ya yankewa Darazo hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda cin amanar aiki da zamba.

Channels TV ta rahoto cewa Darazo dai ya samo takardu biyu daga ofishin sannan ya yi amfani da su wajen bayar da kwangila ga wani kamfani domin su yo wa kungiyar AUPCTRE odar kwamfutoci guda 5,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel