Hukumar kula da aikin 'yan sanda: Rahoton ’yan sanda game da Abba Kyari a cike yake da kura-kurai

Hukumar kula da aikin 'yan sanda: Rahoton ’yan sanda game da Abba Kyari a cike yake da kura-kurai

  • Hukumar kula da ayyukan yan sanda ta ce akwai kura-kurai sosai a rahoton binciken da rundunar yan sandan Najeriya ta gabatar mata kan jami’inta, Abba Kyari
  • A yanzu PSC ta ce ta yi umarnin kafa wani kwamiti na daban domin gudanar da wani bincike tare da cike gibin dake tattare da shi da kuma gabatar mata da sabon rahoto
  • Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, shine ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho

Hukumar kula da ayyukan yan sanda (PSC), a ranar Alhamis, 17 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa rahoton binciken da rundunar yan sandan Najeriya ta gabatar mata kan jami’inta, Abba Kyari, yana cike da kura-kurai da dama.

Hukumar wacce tun farko ta umurci rundunar da ta gudanar da sabon bincike tare da wani kwamiti na daban kan babban jami’in, sannan a gabatar da wani rahoto cikin makonni biyu, ta riki cewa dole a gabatar da sabon rahoto a tsakanin lokacin da ta bayar.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Hukumar kula da aikin 'yan sanda: Rahoton ’yan sanda game da Abba Kyari a cike yake kura-kurai
Hukumar kula da aikin 'yan sanda: Rahoton ’yan sanda game da Abba Kyari a cike yake kura-kurai Hoto: @abbakyari75
Asali: Instagram

Ikechukwu Ani, kakakin hukumar, a wata hira da yayi da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, ya yi bayanin cewa kwamishinonin, karkashin jagorancin Musiliu Smith, Sufeto janar na yan sanda mai ritaya za su dauki sabon hukunci idan kura-kuran suka kara bayyana a sabon rahoton.

A tuna cewa sufeto janar na yan sanda, Usman Baba, ya kafa wani kwamitin bincike domin ya binciki Kyari kan zargin cewa yana da alaka da kasurgumin mai damfara ta yanar gizo, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kwamitin karkashin jagorancin Joseph Egbunike, mataimakin sufeto janar na yan sanda a hedkwatar rundunar, Abuja, ya gabatar da rahotonsa ga IGP, wanda daga bisani aka gabatar da shi ga hukumar PSC.

Bayan bata gamsu da rahoton ba, sai PSC a zamanta na karshe ta mayar da rahoton sannan ta yi umurnin cewa rundunar yan sandan ta kafa wani kwamiti na daban domin binciken lamarin.

Kara karanta wannan

Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi

Amma da yake martani ga tambayan Daily Trust kan ko PSC ta watsar da rahoton farkon, don haka ta nemi ayi sabo, hukumar ta ce bata watsar da rahoton ba, cewa an umurci sabon kwamitin da ya cike gibin da rahoton yake da shi.

Ya ce:

"Watsi? Ba mu yi watsi da rahoton ba. A yanzu dai mun ce akwai bukatar su kara kaimi, akwai kura-kurai, akwai gibi, da ya kamata sabon kwamitin ya magance.
“Idan suka aikata haka sannan suka kawo mana, za mu zartar da hukunci a kan mutumin. Hukumar ta lura akwai gibi, akwai bincike da dama da suka so kammalawa kafin su yanke hukunci kan mutumin. Mun basu makonni biyu su aikata hakan.”

Da aka tambaye shi game da abun da hukumar za ta yi idan aka sake samun kura-kurai a rahoton da za a gabatar mata, Ani ya ce:

“Kun san kuna tambayar abunda ban sani bane. Kun san ni ba mamba bane a hukumar, suna sanar dani jawabai bayan tarukansu. Idan akwai wasu kura-kuran, hukumar za ta duba sannan ta yanke hukunci sannan sai su fada mani.”

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

A gefe guda, mun ji cewa, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da ACP Sunday Ubua da ASP James Bawa daga aiki da mukamansu da ayyukan ofisoshinsu daga ranar Litinin 14 ga Fabrairu, 2022.

Jami’an ‘yan sandan biyu na aiki ne a karkashin DCP Abba Kyari da aka dakatar a cikin tawagar leken asiri ta IRT ta rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Wannan batu dai na kara fitowa ne yayin da ake ci gaba da binciken Abba Kyari da tawagarsa bisa zargin kulla harkallar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel