Da duminsa: Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP

Da duminsa: Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP

  • Kwamitin binciken cin hancin da ake zargin Abba Kyari ya karba daga dan damfara Hushpuppi ya bukaci a rage masa matsayi zuwa ACP
  • Kwamitin ya ce bincikensa ya gano Kyari ya yi karantsaye ga dokokin ayyukan 'yan sanda na taimakawa 'yan damfara
  • A cewar kwamitin, Kyari ya wallafa bayanin kare kansa a Facebook, wanda hakan take doka ce ta aikin 'yan sandan Najeriya

Bayan watsi tare da komawa da binciken a kwamiti na musamman da ke bincikar dakataccen kwamandan IRT, DCP Abba Kyari kan $1.1 miliyan na damfarar da Hushpuppi, da kuma umarnin hukumar kula da ayyukan 'yan sanda na yin sabon bincike, DIG Joseph Egbuniike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi.

Wannan na zuwa ne bayan kwamitin ya tabbatar da cewa Abba Kyari ya hada kai da masu damfara, hakan kuwa ya yi karantsaye ga dokokin ayyukan 'yan sandan Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Da duminsa: Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP
Da duminsa: Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP. Hoto daga Abba Kyari
Asali: Facebook

Baya ga haka, kwamitin binciken ya kama dan sandan da take dokokin soshiyal midiya ta hukumar 'yan sandan Najeriya ta yadda ya yi martani ga tuhumar FBI a shafinsa na Facebook ba tare da ya bi matakan da suka dace ba, wanda daga bisani ya goge martanin.

A bangaren cin hancin da ake zargin an baiwa Kyari, kwamitin ya ce "Shaidun karbar rashawa har yanzu ba gamsassu bane tunda ba a ga yadda kudin suka shiga asusun bankinsa ko kuma yadda suke da alaka da dan sandan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan za a tuna, ofishin antoni janar na tarayya a shawarar da ya bada kan rahoton binciken 'yan sandan, ya bayyana cewa an samu hannun Abba Kyari a damfarar amma rahoton ba shi da karfi kuma ba za a iya amfani da shi a gaban kotu ba, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu, Pantami

Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bada umarnin rufe dukkan sassan rundunar binciken sirri na Intelligence Response Team da Special Tactical Squad a fadin kasar nan.

Wannan na zuwa ne bayan damke dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar IRT na 'yan sandan Najeriya, Abba Kyari da wasu sakamakon zarginsu da ake da harkar safarar miyagun kwayoyi, Channels TV ta rahoto.

Dukkan jami'an 'yan sanda da ke sassa a fadin kasar nan an bukaci da su kai kansu hedkwatar hukumar 'yan sanda da ke Abuja domin karin bayani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel