Wata miyar: Kasa a Afrika za ta fara biyan 'yan zaman kashe wando albashi N41k

Wata miyar: Kasa a Afrika za ta fara biyan 'yan zaman kashe wando albashi N41k

  • Kasa a nahiyar Afrika za ta fara ba matasa 'yan zaman kashe wando albashi duk wata saboda wasu dalilai
  • Kasar ta bayyana adadin kudin da za ta fara ba matasan tare da ba su tallafin kiwon lafiya a kasar baki daya
  • Gwamnatin kasar ta bayyana lokacin da za a fara biyan wannan albashi ga matasan kasar, inda tace watan Maris

Kasar Aljeriya - Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya fada a jiya Talata cewa, gwamnati za ta bullo da tsarin tallafin rashin aikin yi ga matasa yayin da kasar ke fama da rashin ayyukan yi da kusan 15% cikin dari.

Za a biya kudaden ne "domin kiyaye mutuncin matasa," in ji Tebboune a wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Aljeriya, Arab News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yawancin matasan da suka kammala karatun digiri ba sa iya ayyukan da aka basu, Pantami

Shugaban Aljeriya zai fara ba matasa tallafin
Wata miyar: Kasa a Afrika za ta fara biyan 'yan zaman kashe wando albashi N41k | Hoto: arabnews.com
Asali: UGC

Aljeriya za ta ba wa 'yan zaman kashe wando tallafin dinari 13,000 a kowane wata (kimanin Naira 41,000), yunkurin da ke da nufin rage matsalar tattalin arziki, in ji Tebboune ga manema labarai.

Kudin tallafin, wanda ya yi daidai da kusan kashi biyu bisa uku na mafi karancin albashi na dinari 20,000 (akalla Naira 59,000) za a fara ba dashi ne a cikin watan Maris.

Za a dinga biya tare da fa'idodin kiwon lafiya, yayin da kuma za a dakatar da karbar wani nau'in haraji kan kayayyakin masarufi.

Kudin shigan kasar

Aljeriya, kasa ce mai fitar da iskar gas a Afirka mai kusan mutane miliyan 45, tana samun kusan 90% cikin 100% na kudaden shiga daga iskar gas.

Shugaba Tebboune ya ce kudaden da za a fara ba matasa na cikin kasafin kudin 2022.

Kara karanta wannan

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

A watan Nuwamba, 'yan majalisa sun kada kuri'a don soke tallafin da jihohi ke bayarwa kan kayayyakin yau da kullun wadanda suka dade suna taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya, kamar yadda UrduPoint ta tattaro.

Sai dai, hakan ya kawo cikas ga kasafin kudin kasar yayin da kudaden shigar makamashi suka ragu.

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya ya sanar da sabon shirin lamuni ga wadanda suka kammala karatun jami'a da kwalejojin fasaha da ke son kafa kasuwanci, yana mai cewa matakin wani bangare ne a kokarinsa na yaki da rashin aikin yi a kasar.

Bankin ya ce za a aiwatar da shirin lamunin ne a karkashin shirin sa na Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES).

A cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar ta shafinsa na Facebook ya ce:

Kara karanta wannan

Satar Abacha: Najeriya ta dauki Lauya, za tayi shari’a da kasar Birtaniya a kan €180m

“Babban bankin na CBN, a matsayin wani bangare na manufofin sa na magance hauhawar rashin aikin yi ga matasa da zaman banza, ya bullo da Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES) don samar da canji mai kyau tsakanin daliban da suka kammala karatun digiri na kwalejojin kimiyya da jami’o’i a Najeriya, daga neman ayyukan gwamnati zuwa kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel