An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

  • Ana tuhumar matashi da cin zarafin wani mutum ta hanyar tura mishi hotunan tsiraicin matarsa a matsayin hujja na yin lalata da ita
  • Matashin bai tsaya a nan ba, ya cigaba da barazana ga rayuwarta ta hanyar ikirarin yi mata kisan kare dangi
  • Steven Wanjohi Kamande ya bayyana gaban kotun majistare kuma ya musanta laifukan da ake zarginsa da su sannan an bayar da belinsa

Ana tuhumar wani dalibi dan kasar Kenya mai shekaru 21 da zargi kan cin zarafin mijin wata wacce ake zargi da zama masoyiyar sa, bayan ya tura mishi hoton tsiraici na sirrin matar sa.

Wanda ake zargin, Steven Wanjohi Kamande, ya bayyana gaban babban alkalin majistare Wendy Kagendo na kotun shari'a ta Milimani a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta
An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Ya musanta laifuka ukun da ake zargin sa da su, na tura mishi bayanin kanzon kurege, barazana ga rayuwar shi da gangancin yada ababen da basu dace ba.

Kotun ta ji yadda Wanjohi, wanda dalibi ne a wata jami'a a cikin birnin, ya karya doka ta hanyar yada hotunan sirrin, wanda ke nuna Esther Nduta Githinji da niyyar firgita ta da mijin ta Joel Thuo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An zargi wanda ake tuhumar da tura hotunan sirrin matar ga mijinta, a matsayin shaidar yana lalata da ita.

Haka zalika, an tuhume shi da gangancin yada hotunan tsiraici da na sirrin Nduta, matar mutumin da yake korafin wanda ya san ba gaskiya bane, inda ya yada don firgitar wa ga Thuo da iyalin shi.

An zargi wanda ake tuhumar da tura hotunan ta a shafin sa na Facebook a kwanaki daban-daban tsakanin 1 ga watan Mayun 2021 da 14 ga watan Janairun 2022, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata

Takardar dake dauke da karar Wanjohi ta bayyana kalamai kamar haka:

"A kwanaki daban-daban a wurin da ba a ambata ba ta hanyar ganganci an wallafa labarin kanzon kurege, inda aka ce 'unasemanga uki na bibi' ta hanyar amfani da shafin ka na Facebook, Steven Kamande zuwa ga Joel Thuo Mwangi duk da an san ba gaskiya bane, an yada don firgitar wa gami da razanar wa ga Joel da iyalin shi."

An cigaba da tuhumar wanda ake zargin da laifi na uku, na barazanar yi wa Nduta kisan kare dangi, tsakanin lokuta irin wannan a wani wuri da ba a sani ba, cikin Jamhuriyar Kenya bayan bayyanar labarin.

Bayan musanta laifukan da ake tuhumar shi da su, an bayar da belin wanda ake zargin da sharuddan zai cike duk ka'idojin da kotun ta gindaya mishi.

An kuma bukaci ya gabatar da shaidu da za a iya bukata yayin cigaba da sauraron karar shi.

Kara karanta wannan

Wata miyar: Kasa a Afrika za ta fara biyan 'yan zaman kashe wando albashi N41k

Shari'a ba ta haramta sakin shi ba, yayin da kotun Majistaren ta yi umarni da sakin shi tare da biyan Ksh100,000 ko kudin beli kwatankwacin haka da gabatar da mutum daya tabbatacce.

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi

A wani labari na daban, Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.

Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar 'yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel