Karin bayani: Tsohon mashawarcin Tinubu lokacin da yake gwamna ya rasu

Karin bayani: Tsohon mashawarcin Tinubu lokacin da yake gwamna ya rasu

  • Gwamnatin jihar Legas ta yi babban rashi yayin da tsohon mashawarci ga tsohon gwamnan jihar Legas ya riga mu gidan gaskiya
  • Farfesa Tunde Samuel ya yiwa gwamnatin jihar Legas hidima da ma kasa baki daya domin ya rike mukamai
  • Labarin rasuwarsa ya zo ne jiya Laraba, inda rahoto yace marigayin ya rasu yana da shekaru 73 a duniya

Jihar Legas - Wani fitaccen dan majalisar shawara na gwamna (GAC) a jihar Legas Farfesa Tunde Samuel ya rasu.

Ya kasance tsohon mai ba tsohon Gwamna Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin ilimi.

Tsohon mashawarcin Tibunu ya mutu
Innalillahi: Tsohon mashawarcin Tinubu lokacin da yake gwamna ya rasu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

The Nation ta gano cewa Farfesa Samuel ya rasu ne a daren Laraba 16 ga watan Fabrairun 2022, ya rasu yana da shekaru 73.

Kara karanta wannan

Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Da yake makokinsa, kakakin majalisar Legas, Mudashiru Obasa, ya bayyana Farfesa Samuel a matsayin jigo wanda ba za a iya mantawa da kyawawan ayyukansa a Legas ba.

Samuel dai tsohon Farfesa ne a fannin ilimin tattalin arziki kuma tsohon shugaban majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya, Otto-Ijanikin.

Ya rike mukamin Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti da Jami’ar Tarayya da ke Otuoke a Bayelsa.

Allah ya yiwa matar Janar Buba Marwa ta farko, Mrs Zainab, rasuwa

Shugaban hukumar yaki da safara da ta'amuni da muggan kwayoyi NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, ya rasa matarsa ta farko Mrs Zainab Marwa.

A jawabin da iyalan suka saki ranar Asabar, sun ce Zainab Marwa ta mutu ne da safiya bayan gajeriyar jinya da tayi. Ta mutu bayan kwashe shekaru 66 a duniya.

Kara karanta wannan

Ahmad Musa ya yiwa tsohon dan kwallon da ya talauce kyautar N2m

Jawabin ya kara da cewa ta bar 'yaya hudu: Abubakar, Mohamed Jr, Mariam da Zainab, jikoki goma da kuma mahaifiyarta.

Tsufa labari: Tsohuwa mai shekaru 102 ta fito haikan, ta ce ita zata gaji Buhari a 2023

A wani labarin, dattijuwa Iyom Josephine Ezeanyaeche, mai shekaru 102, wacce aka fi sani da Living Legend ko Mama Africa, ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Misis Ezeanyaeche wadda ‘yar asalin karamar hukumar Agwata ce a jihar Anambra ta bayyana aniyar ta ne a lokacin da ake hira da ita a gidan talabijin na NTA tare da mambobin kungiyar Voice for Senior Citizens of Nigeria, wata kungiyar jin kai da ta kafa.

Dattijuwar da ta yi magana ta bakin shugabar kungiyar, Dakta Caro Nwosu, ta ce a shirye ta ke ta tsaya takarar shugabancin kasar idan matasa ba su shirya ba, a cewar wani rahoto da NTA ta gabatar.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa 4 da su ka rike Minista a mulkin Jonathan, yanzu su ne Gwamnonin jihohinsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel