Allah ya yiwa matar Janar Buba Marwa ta farko, Mrs Zainab, rasuwa

Allah ya yiwa matar Janar Buba Marwa ta farko, Mrs Zainab, rasuwa

Abuja - Shugaban hukumar yaki da safara da ta'amuni da muggan kwayoyi NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, ya rasa matarsa ta farko Mrs Zainab Marwa.

A jawabin da iyalan suka saki ranar Asabar, sun ce Zainab Marwa ta mutu ne da safiya bayan gajeriyar jinya da tayi.

Ta mutu bayan kwashe shekaru 66 a duniya.

Jawabin ya kara da cewa ta bar 'yaya hudu: Abubakar, Mohamed Jr, Mariam da Zainab, jikoki goma da kuma mahaifiyarta.

A cewar jawabin, za'a sanar da ranar Jana'izarta daga baya.

Allah ya yiwa matar Janar Buba Marwa ta farko, Mrs Zainab, rasuwa
Allah ya yiwa matar Janar Buba Marwa ta farko, Mrs Zainab, rasuwa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel