Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da nasarar tsagin Shekarau, Ganduje ya samu nasara

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da nasarar tsagin Shekarau, Ganduje ya samu nasara

  • Tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje ta jam'iyyar APC a Kano ta samu nasara a kotun daukaka kara
  • Hukuncin Kotun yanzu ya nuna cewa Abdullahi Abbas Dan Sarki ne sahihin shugaban APC a Kano
  • Mabiya Gwamna GAnduje sun barke da murna a harabar kotun daukaka kara dake Abuja

Abuja - Labarin dake shigo mana da duminsa daga kotun dauaka kara dake birnin tarayya Abuja shine kotun tayi watsi da shari'ar kotun da tayi watsi da zaben tsagin Ganduje.

Zaku tuna cewa babban kotun tarayya ta bayyana zaben shugabannin APC na Kano na tsagin Malam Ibrahim Shekarau a matsayin sahihi.

A yau Alhamis, 17 ga watan Febrairu, kotun daukaka kara tace babbar kotun ba tada hurumin sauraron karar da tsagin Shekarau ya shigar.

Kotun Afil tace lamarin na rikicin cikin jam'yya ne ba na zabe ba, saboda haka uwar jam'iyya ce za tayi sulhu tsakanin yayanta.

Hadimin Gwamna Ganduje kan Soshiyal Midiya, Abubakar Aminu Ibrahim, ya bayyana hakan kai tsaye daga kotun.

APC na Shekarau
Yanzu-yanzu: Kotu daukaka kara ta yi watsi da nasarar tsagin APC na Shekarau Hoto: Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon da Legit ta samu, an ga jami'an gwamnatin jihar Kano suna bayyana farin cikinsu bisa wannan nasara da tsagin Ganduje karkashin Abdullahi Abbas ya samu.

Tsohon dan majalisa, Hanarabul Kawu Sumaila yace:

"Alhamdulillah Allah ya rufa asiri. Yanzu kuma sai jam'iyya ga baki daya APC. A hadu a yiwa jam'iyya aiki."

Hanarabul Musa Kwankwaso yace:

"Kamar yadda kowa ya sani an yanke hukunci kuma Abdullahi Abbas ya zama shugaban jam'iyya dama shine."
"Abinda muke cewa shine kowa yazo. rigima ta kare, karya ta kare."

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa yace:

"Alhamdulillahi, muna godiya. Ubangiji Allah ya tabbatar mana da nasara. Muna kira ga kowa yabi akidar jam'iyyar APC."

Tsagin Shekarau ya yi fatali da yunkurin sulhun uwar jam'iyya

Gabanin hukuncin kotun yau, Uwar jam'iyyar APC ta kasa ta kafa kwamitin mutum 5 na hadin guiwa wanda zai tabbatar da an shirya sabon tsari na magance rikicin jam'iyyar na cikin gida a jihar Kano.

Kwamitin zai samu shugabancin Gwamna Abdullahi Umar ganduje na jihar Kano tare da Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa.

Ganduje da Shekarau ba su ga maciji kan yadda ake tafiyar da al'amuran jam'iyyar a jihar, inda suka rabe tare da fitar da shugabannin jam'iyyar a kowanne tsagi, lamarin da ya sake jefa su cikin rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel