Kano: APC ta kafa kwamitin sulhu, ta nada Ganduje matsayin shugaban jam'iyya

Kano: APC ta kafa kwamitin sulhu, ta nada Ganduje matsayin shugaban jam'iyya

  • Uwar jam'iyyar APC ta kafa kwamitin mutum 5 na sulhu tsakanin fusatattun 'ya'yanta kan rikicin da suke yi a jihar Kano
  • A takardar da uwar jam'iyyar ta fitar, ta ce babu ko shakka Gwamna Ganduje shi ne shugaban jam'iyyar a Kano
  • A kwamitin akwai Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilai da Sanata Abba Ali

Kano - Uwar jam'iyyar APC ta kasa ta kafa kwamitin mutum 5 na hadin guiwa wanda zai tabbatar da an shirya sabon tsari na magance rikicin jam'iyyar na cikin gida a jihar Kano.

Kwamitin zai samu shugabancin Gwamna Abdullahi Umar ganduje na jihar Kano tare da Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa.

Kano: APC ta kafa kwamitin sulhu, ta nada Ganduje matsayin shugaban jam'iyya
Kano: APC ta kafa kwamitin sulhu, ta nada Ganduje matsayin shugaban jam'iyya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ganduje da Shekarau ba su ga maciji kan yadda ake tafiyar da al'amuran jam'iyyar a jihar, inda suka rabe tare da fitar da shugabannin jam'iyyar a kowanne tsagi, lamarin da ya sake jefa su cikin rikici.

Kara karanta wannan

Tsige mataimakin gwamnan Zamfara: Majalisa ta lissafo laifukan Aliyu Gusau

Amma bayan taron sasancin da suka yi a sakateriyar jam'iyyar ta kasa tare da dukkan fusatattun 'ya'yan jam'iyyar, an fitar da wani tsari a daren Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan na kunshe ne a wata wasika da aka fitar ta hade kan dukkan tsagin jam'iyyar a jihar wacce aka aikewa Gwamna Ganduje kuma shugaban ma'aikatan kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar na kasa, Abdullahi Gashua ya saka hannu.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da Sanata Abba Ali da kuma wakilci daga sakateriyar jam'iyyar ta kasa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ana tsammanin kwamitin zai zauna a Kano kuma cikin kwanaki bakwai za a kammala sasancin tare da mika rahoto ga uwar jam'iyyar.

A cikin takardar, dukkan masu ruwa da tsaki da ke taron sun sakankance cewa Ganduje shi ne shugaban jam'iyyar a Kano kuma ana tsammanin a matsayinsa na shugaba zai bayyana halin shugabanci na kwarai ta hanyar hakuri da dukkan masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi

Ganduje ya ziyarci shugaban APC na tsagin Shekarau, Ahmadu Danzago

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Lahadi, ya kai ziyarar ta'aziyya ga shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Ahmadu Danzago, wanda ya karba kujerar a kotu.

Ya kai wa Danzago ziyarar ne sakamakon mutuwar da da yayansa ya yi a ranar Asabar, Premium Times ta ruwaito.

An zabi Danzago a matsayin shugaban APC a jihar a zaben da aka yi na ranar 18 ga watan Oktoba, 2021 wanda tsagin tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel