Yan banza bakwai dama karya suka shuka: Cewar Ganduje bayan nasara a kotun daukaka kara

Yan banza bakwai dama karya suka shuka: Cewar Ganduje bayan nasara a kotun daukaka kara

  • Gwamna Ganduje ya yi murnar nasarar tsaginsa a kotun daukaka kara ranar Alhamis a Abuja
  • Ganduje yace tsagin G7 tun asali kan karya suka shuka kararsa saboda haka babu yadda za'ayi su samu nasara
  • Tsagin Shekarau sun lashi takobin daukaka kara kotun koli

Abuja - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya yi jawabinsa na farko tun bayan nasarar da tsaginsa ta samu a kotun daukaka kara ranar Alhamis, a birnin tarayya Abuja.

Tsakiyar manyan jami'an gwamnati da hadimansa a gidan hutun jihar Kano dake unguwar Asokoro Abuja, Ganduje ya bayyana godiyara bisa al'ummar Kano.

A cewarsa,

"Muna gode wa al'ummar jihar Kano, muna godewa yan jam'iyyar APC...Muna gode wa shugaban riko na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe saboda shi yace mu koma kotu ."

Kara karanta wannan

Da Namiji Ya Kai Shekaru 21 Mazakutarsa Ya Daina Girma, Ku Daina Shan Magani: Likita

Kotun daukaka kara
Yan banza kawai dama karya suka shuka: Cewar Ganduje bayan nasara a kotun daukaka kara Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Ganduje ya kara da cewa yan tsagin tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau watau G7 dusa suka shuka saboda haka ba zasu girbe 'yaya ba.

Yace:

"Idan zaka yi gini, sai ka zo foundation (dasa tubali), sai ka dau toka kasa, sai ka dau bulo kasa, me zai faru da wannan gini? rushewa"
"Mun ga wasu sun debi dussa, sun je suna shuka, wani sakamako za'a samu? Banza bakwai ta shuka dussa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel