Murna ta ɓarke a APC tsagin Ganduje bayan sun lallasa su Shekarau a kotun ɗaukaka ƙara

Murna ta ɓarke a APC tsagin Ganduje bayan sun lallasa su Shekarau a kotun ɗaukaka ƙara

  • Magoya bayan tsagin Gwamna Ganduje na jihar Kano sun fada tsananin shagali da murna bayan kotun daukaka kara ta bayyana hukuncinta
  • An ga jama'ar a Abuja sun fada shagali tare da bidiri, hakazalika a Kano an ga magoya bayan suna ta murna tare da daukar hotuna
  • Alkalai uku na kotun daukaka karar da ke Abuja sun yanke hukuncin yin fatali da hukuncin babbar kotun tarayya wanda aka bai wa su Shekarau nasara

An samu gagarumin murna da shagali a kotun daukaka kara da ke reshen Abuja yayin da kotun ta karba daukaka karar tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Magoya bayan masu murna an gansu suna ihu tare da daga hannu da daukar hotuna. Majiyoyi sun ce wannan shagalin har a cikin Kano an yi shi bayan hukuncin kotun na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Cin amanar aiki: An daure jami'in gwamnati bisa bada kwangilar bogi a jihar Bauchi

Murna ta ɓarke a APC tsagin Ganduje bayan sun lallasa su Shekarau a kotun ɗaukaka ƙara
Murna ta ɓarke a APC tsagin Ganduje bayan sun lallasa su Shekarau a kotun ɗaukaka ƙara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Kwamitin masu shari'ar na kotun daukaka karar da ya samu shugabancin mai shari'a Haruna Tsammani, a ranar Alhamis ya soke hukuncin babbar kotun tarayya wanda aka shigar domin kalubalantar zaben shugabannin jam'iyya na gundumomi da kananan hukumomi.

Kotun daukaka karar da ke zama a Abuja ta yi fatali da hukuncin kotun wanda ya bai wa tsagin Sanata Ibrahim Shekarau nasara kan tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Daily Trust ta tattaro cewa, kotun daukaka karar ta yanke hukunci wanda ya yi wa tsagin gwamnan dadi a dukkan daukaka karar uku da aka mika wa kotun daga karamar kotun.

Hukuncin kotun an bayyana ta ne a safiyar Alhamis ta bakin Masu shari'a Haruna Tsammani, B. I. Gafai da J. Amadi.

"An yi watsi da hukuncin kotun tarayya sakamakon rashin karfin ikon kotun na sauraron karar kuma saboda lamarin ciki gida ne jam'iyyar. Dalili na uku shi ne ko hanyar da aka bi aka shigar da karar ba a yi ta daidai ba kuma hakan yasa aka yi watsi da karar. Wannan hukuncin dukkan alkalan uku sun aminta da shi," Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kano, Barista Lawan Musa ya sanar da Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da nasarar tsagin Shekarau, Ganduje ya samu nasara

Rikicin APC a Kano: Tsagin Shekarau ya yi fatali da yunkurin sulhun uwar jam'iyya

A wani labari na daban, rikici na cigaba da rincabewa na shugabancin jam'iyyar APC a jihar Kano. Bangaren Sanata Shekarau sun yi fatali da sanarwar da uwar jamiyya ta bayar na yunkurin sasanta su.

Babu shakka wannan boren da tsagin Shekarau ke yi ya na da alaka da yadda aka jagorantar da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar a kwamitin sulhun.

A wata tattaunawa da BBC ta yi bayan fitar sanarwar uwar jam'iyyar, Sanata Shekarau ya ce sun yi fatali da sanarwar kuma ba su aminta da ita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel