Sojojin Najeriya Sun Yi Raga-raga Da Sansanin 'Yan Ta'adda a Zamfara

Sojojin Najeriya Sun Yi Raga-raga Da Sansanin 'Yan Ta'adda a Zamfara

  • Rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar ragargazar sansanin ‘yan bindiga da ke dajin Totsari da Kenkashi a karamar hukumar Tsafe cikin Jihar Zamfara
  • Mazauna Mada ne suka sanar da manema labarai hakan a ranar Laraba, inda suka ce lamarin ya auku ne yayin da sojojin suka kai samame kauyen Getawa, Unguwan Kade da kauyen Maigalma
  • A cewar majiyar, yayin da ‘yan bindiga suka nemi tserewa daga sojoji, sun yasar da babura da shanu da suka sace inda sojojin suka bisu suna ta harbin su

Jihar Zamfara - Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation Hadin Kai ta lalata sansanin ‘yan bindiga da ke dajin Totsari da Kenkashi a karamar hukumar Tsafe cikin Jihar Zamfara.

A ranar Laraba wata majiya cikin mazauna Mada ta sanar da Channels TV cewa a ranar Talata rundunar Operation Hadin Kai ta kai samame kauyen Getawa, Unguwan Kade da kauyen Maigalma inda ta ci karo da ‘yan bindigan sun koro shanun da suka sace.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

Sojojin Najeriya Sun Yi Raga-raga Da Sansanin 'Yan Ta'adda a Zamfara
Sojojin Najeriya Sun Lalata Sansanin 'Yan Ta'adda a Zamfara. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar ta shaida:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yayin da ‘yan bindigan suke kokarin tserewa daga rundunar sojojin sun bude musu wuta daga nan suka saki shanun satar suka fara gudu. Take anan sojojin suka bi su suna harbi.
“Sakamakon samamen, an halaka dan ta’adda daya sannan an kwato babura da shanaye da dama da suka sace.”

Sojojin sun gano wani sansanin ‘yan bindigan

Majiyar ta ci gaba da bayyana yadda sojojin suka gano sansanin ‘yan bindigan da ke kauyen Kenkashi da Tostari inda suka yi musayar wuta da ‘yan ta’addan wadanda bayan jin ragargaza suka tsere cikin daji.

Ya kara da cewa:

“Sojojin sun bincike sansanin tsaf inda suka lalata shi sannan yanzu haka sun mamaye kauyakun suna ci gaba da bincike ko ina.”

Wata majiya daga sojojin da ke karamar hukumar Tsafe wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar wa Channels TV aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bindige Mutum Ɗaya, Sun Sace Wasu 10 a Tashar Jirgin Ƙasa a Kogi

Sojojin kasa da na sama suka hada kai wurin tarwatsa ‘yan ta’addan

A cewar majiyar, rundunar Operation Hadarin Daji da sojojin sama sun afka wa sansanin shugaban ‘yan bindigan nan, Hamza Dogo da ke kauyen Busha cikin karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara ranar Lahadi.

Ya bayyana yadda Hamza Dogo da yaransa suka addabi mazauna Tsafe da Mada, kuma farmakin da sojojin suka kai ya tarwatsa sansanin su.

‘Yan bindiga sun addabi karamar hukumar Tsafe da farmaki, don kusan kullum sai sun halaka jama’a tare da garkuwa da wasu.

Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai

A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel