Gallazawa al'umma: Gwamnatin Ganduje ta yi ram da manajojin da ke kara farashin man fetur a Kano

Gallazawa al'umma: Gwamnatin Ganduje ta yi ram da manajojin da ke kara farashin man fetur a Kano

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama manajojin gidajen man fetur hudu bisa zargin sayar da mai fiye da farashin da aka kayyade na N165 kan lita
  • Har ila yau hukumar ta kama ma'aikatan gidajen mai biyu kan lamarin
  • An kama su ne bayan samun korafe-korafe daga jama'a cewa duk da karancin man da ake fama da shi wasu gidajen mai na sayarwa kan N200 zuwa N208 a jihar

Hukumar da ke karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), ta yi ram da wasu manajoji hudu da ma’aikatan mai guda biyu kan siyar da man fetur sama da farashin lita na N165 a jihar.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, mukaddashin shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe, ya ce an kama mutanen ne a gidajen mai mabanbanta da ke cikin garin Kano.

Kara karanta wannan

An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta

Gallazawa al'umma: Gwamnatin Ganduje ta yi ram da manajojin da ke kara farashin man fetur a Kano
Gallazawa al'umma: Gwamnatin Ganduje ta yi ram da manajojin da ke kara farashin man fetur a Kano Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Dalilin kama manajojin

A cewarsa, hukumar ta samu korafe-korafe daga mazauna cewa duk da karancin man fetur, wasu gidajen mai suna siyarwa tsakanin N200 da N208 a jihar, rahoton BBC Hausa.

Mista Balarabe ya ce bayan sun samu korafe-korafen, sai hukumar ta shiga aiki sannan ta je wasu gidajen mai a kwaryar birnin da hanyar Hadejia, inda ta gano wasu daga cikinsu su na sayar da mai a kan N200 da N208 a ko wacce lita.

Daily Nigerian ta nakalto Balarabe yana cewa:

“A yayin aikin, mun kama manajojin gidajen mai hudu. An kama mutum daya a lokacin da yake taimakawa manajan gidan mai wajen canja litar sama da N165.
“Daya mutumin kuma ma’aikacin mai ne kuma mun kama shi ne bayan manajan nasa ya haura katanga ya gudu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

“Akwai gidan mai da muka gano cewa sun rigada sun siyar da lita 18,000 kan N200, inda suka samu N630,000 a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. An gano dayan gidan mai ya boye sama da lita 4,000. Mun tursasa su ci gaba da sayar wa mutane lita 4,000 da su ka boye.”

Mista Balarabe, wanda ya nuna fushinsa kan lamarin, ya ce hukumar za ta binciki wadanda ake zargin tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki.

Ya koka kan cewa duk da sake farfado da layukan mai a jihar, manajojin gidajen man na ci gaba da gallazawa mutane ta hanyar canja litar man fetur sama da farashin da aka kayyade na N165.

Ya kuma sha alwashin cewa hukumar ba za ta lamunci abin da ya suffanta da “ayyukan cin hanci da rashawa” ba, inda ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da sumamen har sai ta kawar da duk wani abu da bai dace ba a tsakanin jama’a.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya magantu kan wadanda suka shigo da gurbataccen man fetur, ya sanar da matakin dauka

'Dan-karen wahalar mai ya sa farashin fetur ya tashi da kusan 150%, lita ta kai har N400

A gefe guda, mazauna Abuja da yankin jihohin Neja da Nasarawa su na fuskantar wahalhalu a sanadiyyar wahalar man fetur. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Rahoton da aka fitar a safiyar yau Litinin ya bayyana cewa har ta kai mutane su na sayen litar man fetur a kan N400 a hannun ‘yan bumburutu a halin yanzu.

Samun man fetur a birnin tarayya Abuja da kewaye sai a wajen ‘yan bumburutu a halin yanzu, wadanda suke saida mai a cikin robobi da ‘dan karen tsada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel