Da duminsa: Buhari ya magantu kan wadanda suka shigo da gurbataccen man fetur, ya sanar da matakin dauka

Da duminsa: Buhari ya magantu kan wadanda suka shigo da gurbataccen man fetur, ya sanar da matakin dauka

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin hukunta duk mai hannu a shigowa tare da siyar da gurbataccen man fetur
  • Cike da damuwa da lamarin, Buhari ya bai wa hukumomin gwamnati umarnin daukar mataki kan masu cuta a kasuwa tare da rashin adalci
  • Kamar yadda takardar da Garba Shehu ya fitar ta bayyana, shugaban kasan ya ce dole ne a bai wa jama'a kariya daga masu almundahana a kasuwa

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin hukunta wadanda suka samar tare da shigo da gurbataccen man fetur kasar nan.

Shugaban kasan ya bayar da wannan umarnin ne a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun Garba Shehu, babban mai bada shawara na musamman ga shugaban kasan a harkar yada labarai.

Kara karanta wannan

Gurbataccen man Fetur: FG na iya mayar da mai ga masu kawo shi, abun ya shafi lita miliyan 100 - Yan kasuwa

Da duminsa: Buhari ya magantu kan wadanda suka shigo da gurbataccen man fetur, ya sanar da matakin dauka
Da duminsa: Buhari ya magantu kan wadanda suka shigo da gurbataccen man fetur, ya sanar da matakin dauka
Asali: Original

TheCable ta ruwaito cewa, kamar yadda shugaban yace, duk mai hannu a wannan lamarin dole ne a hukunta shi kan almundahana da kuma shigo da kaya maras kyau tare da siyarwa.

Shugaban kasar ya umarci hukumomin gwamnati da suka dace da su dauka duk matakin da yayi daidai da dokar kasar nan wurin tabbatar da an mutunta tare da bai wa jama'a kariya daga masu almundahana a kasuwa da rashin adalci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai

A wani labari na daban, yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ta kowane bangare, wasu masu gidajen mai suna kara wa ciwon gishiri ta hanyar sayar da gurbataccen mai.

Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana lokacin da wani ma'aikacin gidan mai ke kokarin cika wata gorar ruwa da wani mai launin ja da ya yi kama da gurbatacce.

Kara karanta wannan

Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a kan shafin Facebook na jaridar Punch, an ga man da ake dura wa gorar da launin da bai yi kama da na man fetur ko kalanzir ko gas ba, duk da cewa a gidan mai ne.

Hakazalika, jaridar ta shaida cewa, wannan bidiyon ya fito ne daga jihar Legas, amma har yanzu ba a gano wane gidan mai bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel