2023: Tsohon ɗan majalisa ya bayyana tushen gagarumar dukiyar Bola Tinubu

2023: Tsohon ɗan majalisa ya bayyana tushen gagarumar dukiyar Bola Tinubu

  • Daraktan kungiyar kamfen din Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana tushen gagarumar dukiyar Tinubu da ake ta cece-kuce a kai
  • Jibrin ya sanar da cewa Tinubu tun kafin ya shiga siyasa mai tarin arziki ne domin ya yi aiki da kamfanin Mobil da wasu manyan kamfanoni
  • Ya bayyana cewa, jama'a za su yi mamaki idan ya sanar da cewa Tinubu ya na da hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United

Bayan daukan tsawon makonni ya na kauce wa tambaya game da tushen arzikin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, babban daraktan kungiyar goyon bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin, daga karshe ya bayyana wa duniya sirrukan.

Yayin tattauna wa da TVC News, an kara tambayar Jibrin, tsohon dan majalisar dattawa, game da tushen arzikin Tinubu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya naɗa ɗan shekaru 31 a matsayin shugaban watsa labaransa na ƙasa

2023: Tsohon ɗan majalisa ya bayyana tushen gagarumar dukiyar Bola Tinubu
2023: Tsohon ɗan majalisa ya bayyana tushen gagarumar dukiyar Bola Tinubu. Hoto daga @tvcnewsng
Asali: Twitter

Ya ce, tushen arzikin shugaban Jam'iyyar APC ta kasa bai taba zama dalilin tada kura ba,inda yace hakan abu ne bayyananne.

Kamar yadda tsohon dan majalisar ya ce, kungiyoyin kasashen duniya sun dade suna bibiyar Tinubu tun daga rayuwar da yayi a makaranta, inda ya ce, tsohon gwamnan Legas din yayi aiki a kamfanin Mobil da wasu kamfanoni kafin ya fada siyasa. Jibrin ya kara da bayyana cewa Tinubu bai shigo siyasa a fakiri ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Zan iya tabbatar muku da cewa, duk sanatocin Najeriya babu talaka, kuma ya shigo siyasa a matsayin sanata. Yana da hanyoyin samun kudi," yace,
"Mutumin nan kasuwanci a jinin sa yake. Ya na kasuwanci tsakanin kasa da kasa. Duk mutanen da ke cece-kuce game da shi sun sani sarai cewa yana daukan nauyin hidindimun siyasar sa ba tare da wani ya tallafa mishi ba tun a tsakiyar karni na 19.

Kara karanta wannan

Shugabancin ƙasa a 2023: Daga ƙarshe an bayyana inda Tinubu ya samo arzikinsa

"Saboda haka, meyasa basu tambayar inda yake samo kudin? Wannan wani mutum ne da ya zuba hannun jari a ko ina a fadin duniya.
"Ni abun mamaki ya bani, lokacin da muna kallon kwallo tare...da na gano cewa yana da hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Dama tuntuni yana kasuwanci.
"Idan aka ajiye wannan a gefe, mutum mai matsayi irin nashi, matakin da ya kai a siyasa, ba a Najeriya kadai ba, a duk fadin duniya, dan siyasa mai matsayin Asiwaju ya samu nasarori daban-daban.
"Saboda haka za a iya cewa tushen arzikin Tinubu daga kasuwanci da yake, aikin da yayi da kuma tarin mosoyan shi, hakan bai kamata yazo wa mutane a abun mamaki ba," ya kara da cewa.

Shugaban kasa a 2023: Shettima ya bayyana abun da arewa ba za ta iya yiwa Tinubu ba

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce yanzu ne lokacin da arewa za ta marawa kudirin takarar shugabancin kasa na babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Jagoran Win/Win Mu'az Magaji ya nemi a sassauta masa sharuɗan belin da aka sanya masa.

A wata hira da jaridar Daily Trust, Shettima ya ce lallai lokaci ne na sakawa Tinubu wanda ya tabbatar da ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cimma dadaddiyar burinsa.

Ya ce da taimakon jigon na APC ne Buhari ya yi nasarar kayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben na 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel