Innalillahi: Wani Mutum Ya Kashe Maƙwabinsa Saboda Bokitin Ruwa a Kaduna

Innalillahi: Wani Mutum Ya Kashe Maƙwabinsa Saboda Bokitin Ruwa a Kaduna

  • Wani mutum mai suna Gado Yahaya ya yi sanadin salwantar ran makwabinsa mai suna Liman Salisu ta hanyar buga masa tabarya a kai
  • Yahaya ya buga wa Salisu tabaryan ne yayin da suke rikici game da bokitin ruwa a unguwar Rigasa Kaduna kamar yadda ganau ya fadi
  • Alkalin kotun majistare a Kaduna ya ce ba za a saurari shari'ar ba a yanzu domin kotunsa ba ta da hurumin sauraron karar ya kuma bada umurnin a tsare Yahaya a gidan gyaran hali

Kaduna - An gurfanar da wani tela mazaunin Kaduna, Gado Yahaya a gaban kotun majistare a ranar Litinin kan zarginsa da kashe makwabincinsa yayin rikici kan bokitin ruwa a Kaduna.

Yahaya ya shaida wa kotun majistaren na Kaduna cewa shekarunsa 29, kuma yana cike da nadama a kotun, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Innalillahi: Wani Mutum Ya Kashe Maƙwabinsa Saboda Bukitin Ruwa a Kaduna
Wani ya kashe makwabcinsa saboda bokitin ruwa a Kaduna. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin Rigasa, garin da telan ke zaune, ya ce Yahaya sun yi dambe da Liman Salisu yayin musu kan bokitin ruwa hakan ya yi sanadin rasuwar Salisu.

Ya ce:

"Mazaunin Rigasa ne a Jihar Kaduna kuma an gurfanar da shi ne kan zargin kisa a gaban Kotun Majistare a Kaduna a ranar Litinin.
"Mai gabatar da karar, Sifeta Chidi Leo ya yi ikirarin cewa Yahaya ya kashe Salisu da tabarya ne yayin da suke fada kan bokitin ruwa.
"A yayin fadar, ya shiga kitchen, ya dako tabarya ya buga wa Salisu a kai. Ya yanke jiki ya fadi bayan buga masa tabaryar a kai, ya mutu a hanyar mu na zuwa asibiti."

A cewar Mr Leo, Mai gabatar da karar, Yahaya ya rubuta cewa ya aikata hakan ya kuma saka hannu a lokacin da aka kawo shi ofishin yan sanda don masa tambayoyi, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Ɗa ya doke mahaifinsa da taɓarya, ya aike shi barzahu a jihar Yobe

Laifin, ya ce, ta saba wa sashi na 190 na dokar Penal Code ta Jihar Kaduna, ta 2017.

Kotu ta dage fara sauraron shari'a zuwa watan Maris

Amma, kotun ta umurci yan sandan su mika takardan shari'ar zuwa ofishin direkta na shari'a a jihar domin a bada shawara sannan ya ce za a fara sauraron karar a Maris na 2022.

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bada umurnin a tsare Yahaya a gidan gyaran hali kuma ya ki sauraronsa kan cewa kotun ba ta da hurumin yin shari'ar.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani labarin, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel