Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa

Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa

  • Alkali Abdullahi Sigil a Adamawa ya aike wani mai goyon bayan Atiku Abubakar gidan yari bayan zundumawa Lamidon Adamawa zagi da yayi
  • An gano cewa Baban Yola sun samu hargitsi ne da wani mai goyon bayan Buhari, lamarin da yasa ya kira shi a waya tare da zaginsa har da Barkindo Aliyu Musdafa
  • Masarautar ba ta yi kasa a guiwa ba, ta garzaya kotu inda aka fara shari'ar har da aika Baban Yola gidan maza

Adamawa - Alkali ya aike wani mai goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, zuwa gidan kaso.

An aika Yusuf Baban Yola mai shekaru 43 a duniya gidan yarin ne kan zarginsa da ake da zagin Mai Martaba Lamidon Adamawa, Barkindo Aliyu-Musdafa.

Alkalin kotun majistaren da ke zama a Yola a ranar Litinin ya umarci a tsare Baban Yola a gidan yari bayan 'yan sanda sun gurfanar da shi saboda korafin masarautar.

Kara karanta wannan

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa
Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya fara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An zargi cewa Baban Yola ya fusata da wani dan siyasa mai suna Bako DDK, wanda a gidan rediyo ya zargi Atiku da kin taka rawar gani ga rayuwar jama'ar Adamawa yayin da ya ke mataimakin shugaban kasa, Premium Times ta ruwaito.

A shirin makon da ya gabata a gidan rediyon NAS FM, DDK, wanda masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ya bayyana nasarorin da shugaban kasan ya samu kuma ya kalubalanci Atiku da ya fito ya bayyana nashi.

Ya ce shugaban kasa ya yi abinda Atiku bai yi wa jihar ba ko duba da yadda ya dinga bai wa 'yan jihar mukaman siyasa a matakin tarayya.

"Ba kamar tsohon mataimakin shugaban kasa ba, za ku iya bayyana wa wanda ya yi karfi ta sanadinsa a Adamawa? A shirin da ya gabata, na kalubalanci magoya bayan Atiku da su bayyana wani aiki na cigaba da tsohon mataimakin shugaban kasan ya kawo, amma shiru kake ji," DDK yace.

Kara karanta wannan

Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari

Amma bayan shirin, Baban Yola ya kira DDK inda yace masa ya fita daga sabgar Atiku.

A yayin da Baban Yola ya dinga zundumawa DDK zagi, DDK ya ce ya na girmama shi. Ya ce shirin gidan rediyo siyasa ce zalla kuma bai yi maganganunsa domin tozarta kowa ba.

Amma duk da haka, Baban Yola bai hakura ba.

"Ko da mahaifin ka ne Lamidon Adamawa, sai in ci uwar Lamidon. Mu hadu gobe, sai na yi maganin ka ko da kuwa uban ka ne mai bada shawara kan tsaron kasa, ka je Aso Rock ka kai korafina.
"Ai Jimeta kake, nima haka, zan yi maganin ka. Ka ci uwar ka da siyasar ka. Atiku tsaranka ne? Dan ka ne? Zan nuna maka na isa a kasar nan," Fusataccen Baban Yola yace.

Yadda ta kaya a kotun

Bayan wannan rikicin, an gurfanar da Baban Yola a gaban kotun kan zargin aikata laifuka uku da suka hada da cin zarafi a yanar gizo, zagi da kuma tada tarzoma.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

'Yan sanda sun ce Baban Yola ya aikata laifukan da suka ci karo da sashi na 24 na haramcin cin zarafi ta sanar gizo da sashi na 385 da 80 na dokokin Penal Code na jihar.

Dan sandan da binciken ke hannunsa, Iliya Akawu, ya sanar da kwamishinan 'yan sandan jihar ya samu wasika a ranar 5 ga watan Fabrairun daga masarautar Adamawa.

Dan sandan ya bayyana cewa, wasikar ta sanar da yadda a watan Fabrairun Baban Yola ya dinga zagin Lamidon Adamawa a waya, Premium Times ta ruwaito.

Dan sandan ya ce, wanda ake zargin ya yi amfani da miyagun maganganu tare da zagin basaraken.

Alkali Abdullahi Sigil ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 8 ga Fabrairun domin jin bukatar belin Baban Yola da lauyarsa ta shigar.

An daure matashi watanni 9 a gidan yari kan ya zagi gwamna Masari

A wani labari na daban, wata kotun majistri a jihar Katsina ta daure wani matashi mai suna Gambo Saeed daurin watanni 9 a gidan kaso saboda ya zagi gwamnan jihar Aminu Bello Masari a kafar sadarwa na zamani.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Shi dai Saeed mazauni ne a kauyen Muduru na karamar hukumar Mani dake jihar Katsina, kauyen tsohon Kaakakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Sabiu Muduru.

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito Dansanda mai shigar da kara Inspekta Isa Liti yana bayyana ma kotu cewar sun gurfanar da Saeed ne sakamakon korafi da suka samu daga mashawarcin gwamnan jihar Katsina ta fannin sa’ido a gidajen rediyo Mansur Ali Mashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel