Jerin abubuwa 12 da ka iya yuwu wa baku sani ba game da DCP Abba Kyari

Jerin abubuwa 12 da ka iya yuwu wa baku sani ba game da DCP Abba Kyari

  • A yau Litinin, yan sanda suka kama DCP Abba Kyari, kuma suka miƙa shi hannun NDLEA bisa zargin safaran muggan kwayoyi
  • Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa 12 da ka iya yuwu wa baku san su ba game da gwarzon ɗan sandan
  • Hukumar NDLEA ta saki bayanan dake nuna Kyari na tayin makudan kuɗi domina sakar masa Hodar Ibilis

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a ranar Litinin, ta fitar da wasu bayanai game da shugaban tawagar fasaha IRT, Abba Kyari.

The Nation ta rahoto cewa NDLEA ta fitar da wani faifan Bidiyo dake nuna mataimakin kwamishina, Kyari, wanda aka dakatar yana baiwa jami'inta cin hanci domin sakar masa Hodar Ibilis.

Mun tattaro muku wasu abubuwa 12 game da Abba Kyari, wanda ka iya yuwu wa baku san da su ba. Ga su kamar haka:

Kara karanta wannan

Kannywood: Muhimman Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game Naziru Sarkin Waka

DCP Abba Kyari
Jerin abubuwa 12 da ka iya yuwu wa baku sani ba game da DCP Abba Kyari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

1. An haifi Abba Kyari a ranar 17 ga watan Maris, 1975.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Kyari ya kai matakin mataimakin kwamishinan yan sanda kuma ɗaya daga cikin mambobin tawaga IRT ta Sufetan yan sanda na ƙasa.

3. Haka nan, shi Mamba ne a ƙungiyar shugabannin yan sanda ta ƙasa da ƙasa (IACP).

4. Gabanin naɗa shi shugaban tawagar IRT, Kyari ya yi aiki a hukumar yan sanda reshen jihar Legas a matsayin shugaban yan sandan SARS.

5. Sunan Abba Kyari ya shahara ne a Najeriya bayan ya samu nasarar damƙe hatsabiban shugabannin masu garkuwa da mutane, Evans da Wadume da sauran su.

6. Abba Kyari ya samu gurbin karatu a makarantar yan sanda dake Wudil jihar Kano a shekarar 2000.

7. Ya kammala makarantar a matsayin ASP kuma hukumar yan sanda ta tura shi jihar Adamawa yin aikin shekara ɗaya na horon sanin makamar aiki a Song Police Division.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

8. Daga baya aka maida shi DCO kuma aka tura shi Numan, jihar Adamawa kuma ya yi aiki a matsayin kwamandan sashi na 14 Yola.

9. Ya koma hukumar yan sandan jahar Legas a matsayin 2 IC kafin daga bisani a maida shi shugaban tawagar yan sandan SARS.

10. A ranar 1 ga watan Agusta, Kyari ya musanta zargin ya nemi kaso ko karɓan cin hanci a hannun fitaccen ɗan damfarar Intanet, Ramon Olorunwa Abbas.

11. A ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022, hukumar NDLEA ta bayyana yadda Abba Kyari ya yi tayin zunzurutun kuɗi $61,400 domin tattauna wa kan Hodar Ibilis mai nauyin Kilo 25kg.

12. DCP Abba Kyari, ya yi aure kuma Allah ya azurta shi da samun 'ya'ya.

A wani labarin kuma An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel