Kannywood: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da Naziru Sarkin Waka

Kannywood: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da Naziru Sarkin Waka

  • Naziru M Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Wakan Sarkin Kano ya ja hankalin masu bibiyar Kannywood a kwanakin nan
  • Mawakin na ɗaya daga cikin fitattun mawakan Hausa, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da shi, da ya kamata ku sani
  • Naziru ya jawo cece-kuce ne bayan zargin alaƙa mara kyau da Matan Kannywood ke yi da wasu jarumai

Kano - Naziru M Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin waka, shi ne jagaba a irin waƙoƙin da yake rera wa na Hausa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Sarkin Waka ya sake gabatar da kiɗan wakokin da amma tare da zamanantar da su, wanda ya sa ake gane shi cikin sauki a wakokin Hausa.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan abubuwa 5 da suka faru da jarumin dan sanda Abba Kyari tun farkon tuhumarsa

Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa biyar da baku dani ba game da fitaccen mawakin.

Sarkin Waka, Naziru M Ahmad
Kannywood: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da Naziru Sarkin Waka Hoto: @sarkin_wakar_san_kano
Asali: Instagram

1. Naziru M. Ahmad ƙani ne ga shahararren mawaƙin nan na Kannywood kuma Jarumi, Musbahu M. Ahmad. Kuma an haife shi ranar 17 ga watan Afrilu, 1985.

2. Tsohon Sarkin Kano da aka tsige, Muhammad Sanusi II, ya naɗa Naziru sarautar Sarkin Wakan Sarkin Kano a watan Disamba, 2018.

3. Sarkin Waƙa ya shahara a kafafen sada zumunta ta fannin nuna alfahari da dukiya. Naziru na nuna yana da motocin Alfarma da dama.

4. Mawakin na da alaƙa ta kusa da shahararren Daraktan Fina-Finan Kannywood, Aminun Saira, kuma yana ɗaya daga cikin ginshiƙan shirin 'Labarina Series' wanda ya fito a cikin shirin.

5. Naziru ya yi ruwa ya yi tsaki a zaɓen 2019 ɓangaren ɗan takarar gwamnan Kano karkashin inuwar jam'iyyar hamayya PDP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida).

Kara karanta wannan

Jerin gaskiya 12 da baku sani ba game da ɗan sanda Abba Kyari da aka damke

Sarkin Waka ya rera wakoki da dama domin nuna tsantsar goyon bayansa ga fitaccen ɗan siyasan na jihar Kano.

A wani labarin kuma An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel