An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

  • Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano
  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa
  • Ana gani abubuwa da dama ka iya ta da zaune tsaye tsakanin al'ummar Kano, matukar Sanusi II ya shigo jihar

Kano - Masana a siyasa da tsaro sun nuna matukar damuwarsu kan shirin tsohon sarkin da aka sauke, Sanusi Lamido, na kai ziyara jahar Kano.

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jiha, waɗan da suka zanta da jaridar Leadership, sun roki tsohon sarkin ya dakatar da shirin zuwa Kano a halin yanzu.

A cewarsu, tsoron da suke shi ne, akwai yuwuwar tada hankulan mutane wanda ka iya sanadin rikici tsakanin masoyan tsohon sarkin da yan adawarsa.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ma'aikacin FG ya tsare matarsa da bindiga, ya nemi ta biya shi kuɗin da ya kashe a kanta

Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido
An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin manyan mutane, kuma babban jami'in tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa yace ra'ayin tsohon sarkin na kai takara Kudu ya fusata wasu kuma zasu iya amfani da zuwansa don tada rikici.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kazalika ya ƙara da cewa duk da sanin kowa ne an tunɓuke shi daga Sarauta, amma yana halartar taruka cikin kayan Sarauta, hakan ka iya jawo matsala saboda akwai Sarki mai ci a Kano.

Ya ce:

"Kowa ya san cewa Sanusi tsohon ɗalibin Kwalejin Legas ne, kuma yana da abokan da suka yi makaranta tare a kudu maso yamma, amma har yanzun ba'a san wanda yake goyon bayan ya gaji Buhari daga yankin ba."
"Kazalika sanin kowa ne Sanusi ya bayyana cewa ya fi son rike muƙamin Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, fiye da shiga neman kujerar siyasa."

Kara karanta wannan

Bayan kwana 2 da sakinsa, Mu'az Magaji ya ziyarci Shekarau, ya ce gwagwamaya yanzu suka fara

Shin gwamnatin Kano ta san da zuwan tsohon sarkin?

A ɓagaren gwamnati, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, yace ba shi da masaniya kan shirin zuwan Sanusi.

Ya ƙara da cewa idan ma jita-jitar gaskiya ce, "Muna maraba da shi, a matsayinsa na. ɗan asalin jihar Kano, yana da damar zuwa jiharsa, gwamnati ba ta da matsala da haka."

Tsohon hadimin Sanusi, Farfesa Auwal Hamisu Yadudu, ya bayyana cewa ba shi da masaniyar zuwan tsohon sarkin Kano.

Farfesa Yadudu yace:

"Ban san zai shigo jihar Kano ba, ba wanda ya sanar da ni wannan shirin, kuma ina da yaƙinin cewa idan zai shigo ina daga cikin waɗan da za'a gaya wa."

A wanani labarin kuma Shugaba Buhari ya watsa wa gwamnonin APC biyu ƙasa a ido, ya ƙi amincewa da bukatarsu

Shugaba Buhari ya watsa wa wasu gwamnonin APC biyu ƙasa a Ido, ya umarci su bi matakai matukar suna son ya amince.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Rahoto ya nuna cewa gwamnonin sun garzaya ga Buhari ne domin ya goyi bayan ɗan takarar da suke so ya zama shugaban APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel