'Karin Bayani: Abdulmalik Tanko ya musanta sace Hanifa, da kashe ta

'Karin Bayani: Abdulmalik Tanko ya musanta sace Hanifa, da kashe ta

  • Malamin makarantar su Hanifa Abubakar, Abdulmalik Tanko ya musanta zargin da ake masa na kashe dalibar mai shekaru 5 a Kano
  • Ya bada wannan amsar ne bayan karanto masa tuhume-tuhume biyar da suka hada da zargin hadin baki, garkuwa da mutum, boye wanda aka yi garkuwa da ita da kuma kisa
  • Abdulmalik Tanko da Hashimu Isiyaku sun amince da tuhumar hadin baki yayin da Fatima Jibrin ta musanta dukkan zargin da ake mata

Kano - Abdulmalik Tanko, malamin makaranta da ya bayyana cewa ya sace dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar, kuma ya kashe ta, ya musanta zargin kisan kai da ake tuhumarsa da shi.

Daily Nigerian ta rahoto cewa gwamnatin Jihar Kano ta shigar tare da tuhuma biyar a kan Tanko da wadanda suka taimaka masa, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin, a babban kotu na 5 a jihar.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Yanzu-Yanzu: Abdulmalik Tanko ya musanta sace Hanifa, da kashe ta
Abdulmalik Tanko ya musanta sace Hanifa, da kashe ta. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gurfanar da su uku kan zargin hadin baki, garkuwa da mutum, boye wa/tsare wanda suka yi garkuwa da ita da kuma kisa, wanda sun ci karo da sashi na 97, 274, 277 da 221 na Penal Code.

Abdulmalik da Hashimu sun musanta dukkan zargin illa hadin baki

Da aka karanto musu tuhumar da ake musu a ranar Litinin, Abdulmalik da mutum na biyu da ake tuhuma, Hashimu Isiyaku, sun musanta tuhume-tuhumen sai dai na farkon kawai na hadin baki don aikata laifi.

Fatima Jibrin ta musanta dukkan zargin da ake mata

A bangarenta, mutum na uku da ake tuhuma, Fatima Jibrin ta ce bata aikata dukkan abin da ake tuhumarta da shi ba kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Bisa dogaro da sashi na 36(6b) na kundin tsarin mulkin kasa ta 1999, lauyan wadanda ake zargi, ML Usman, ya bukaci a bashi dukkan bayanai game da shari'ar don ya shirya yin shari'a cikin sati daya.

Kara karanta wannan

Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka matar aure, sun raunata 'ya'yanta 2

Alkalin kotun, ya amince da bukatar ta lauyan wadanda ake zargin ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 2 da 3 ga watan Maris.

Ya kuma bada umurnin a cigaba da tsare su a gidan gyaran hali.

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel