Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka matar aure, sun raunata 'ya'yanta 2

Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka matar aure, sun raunata 'ya'yanta 2

  • An tsinta gawar wata matar aure a cikin gidanta bayan miyagun sun shiga tare da halaka ta da tabarya a yankin Dambare da ke Kano
  • Har a halin yanzu ba a san wadanda suka aikata mugun aikin ba, saboda mijinta ya koma gida ne ya tarar da ita kwance cikin jini
  • Miyagun sun lakadawa 'ya'yanta biyu mugun duka inda dan shekara uku daga ciki ya ke asibiti bai san inda kanshi yake ba

Kano - Rukayya Mustafa matar aure ce mai shekaru 24 da aka shiga har gida aka halaka ta a yankin Dambare da ke jihar Kano.

Yankin Dambare ya na daga cikin yankunan da ke da makwabtaka da sabuwar jami'ar Bayero da ke Kano wacce ke kunshe da yawan daliban jami'ar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai

Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka mata aure, sun raunata 'ya'yanta 2
Kano: Miyagu sun shiga har gida sun halaka mata aure, sun raunata 'ya'yanta 2. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

City & Crime ta tattaro cewa matar da aka kashe har lahira an samu gawarta ne a gidanta da daren Asabar yayin da mijinta ba ya gida.

Miyagun sun nada wa 'ya'yanta biyu masu shekaru uku da daya dukan tsiya.

A yayin zantawa da City and Crime, kawun wacce aka kashen mai suna Kasim Ahmed, ya ce ya samu kiran gaggawa daga mijin wacce aka kashe wurin karfe 9 inda ya sanar masa aukuwar lamarin kuma suna hanyarsu ta zuwa asibitin Murtala inda aka tabbatar da mutuwarta.

"Ni ne waliyyinta, ni na bayar da auren ta. An kira ni yayin da nake gida aka sanar da ni cewa an kashe ta.
"A lokacin da na isa, na ganta a cikin mota kwance a mace. Har yanzu ba a san wadanda suka yi aika-aikar ba saboda a dakinta aka ganta kwance cikin jini. Allah ne kadai ya san abinda ya faru saboda jininta a daskare aka gani a jikinta.

Kara karanta wannan

Zargin kona Al-Kur'ani: Fusatattun jama'a sun babbaka wani mutum a Pakistan

"Abu na biyu, hannayenta sun kandare kuma ba su iya mikewa. Don haka babu wanda ya san abinda ya faru. Mijinta Jamilu Abdulkadir ne ya fara ganinta a cikin wannan halin yayin da ya koma gida da dare.
"Akwai tabarya wacce miyagun suka buga mata a kanta. Sun buge ta wurare biyu daban-daban. Sun doke dan ta mai shekaru uku da tabaryar wanda a halin yanzu bai san inda kanshi ya ke ba.
"Yaranta biyu ne kuma dayan shekararsa daya da watanni kadan."

Kamar yadda BBC ta ruwaito, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar mummunan lamarin inda tace tana bincike a kai.

Ke duniya: Ɗa ya doke mahaifinsa da taɓarya, ya aike shi barzahu a jihar Yobe

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Yobe a ranar Laraba ta ce wani matashi mai shekaru ashirin a duniya mai suna Mai Goni, ya halaka mahaifinsa mai suna Goni Kawu har lahira.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Mummunan al'amarin ya auku ne a garin Masaba da ke karamar hukumar Bursari ta jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata wurin karfe bakwai da rabi na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel