1999 zuwa 2022: Jerin lokutan da ASUU ta shiga yajin aiki, da adadin kwanakin da ta yi

1999 zuwa 2022: Jerin lokutan da ASUU ta shiga yajin aiki, da adadin kwanakin da ta yi

  • Yayin da aka tsunduma yajin aikin ASUU na 2022, dalibai za su so sanin yadda ASUU ta fafata da yajin aiki
  • Tun shekarar 1999 ASUU ta fara yajin aiki saoda wasu dalilai da ba sa yiwa kungiyar dadi tsakaninta da gwamnati
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku adadin kwanaki da lokutan da ASUU suka yi yajin daga 1999 zuwa 2020

Najeriya - Rahoton Punch ya ce ASUU ta shiga yajin aiki. Yayin da kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta shiga yajin aiki a yanzu, dalibai za su san na yi domin ba a san adadin ranakun da kungiyar za ta yi ba kafin ta dawo.

Daga shekarar 1999 zuwa 2020, kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki sau 15, lamarin da ya jawo tsaiko ta wasu bangarorin ilimi ga daliban jami'a.

Kara karanta wannan

A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki

Yajin aikin ASUU daga 1999 zuwa 2022
1999 zuwa 2020: Jerin lokutan da ASUU ta shiga yajin aiki, da adadin kwanakin da ta yi | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A duk wadannan lokuta, ASUU na samun tasgaron wata bukata ce daga gwamnatin tarayya, wanda ya rage mata babu zabin da ya zarce shiga yajin aiki domin neman sulhu cikin sauki.

A yau, 14 ga watan Fabrairu, kungiyar ta sake shiga wani yajin saboda gazawar gwamnatin wajen biya mata bukata kamar yadda aka saba, inji ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Teburin jerin yajin aikin ASUU

legit.ng Hausa, ta tattaro daga majiya lokutan da ASUU ta shiga yaji tun daga 1999 har zuwa 2020, kamar yadda The Cable ta tattara.

Ga jerin kamar haka:

  1. Shekarar 1999 - Kwanaki 150
  2. Shekarar 2001 - Kwanaki 90
  3. Shekarar 2002 - Kwanaki 14
  4. Shekarar 2003 - Kwanaki 180
  5. Shekarar 2005 - Kwanaki 14
  6. Shekarar 2006 - Kwanaki 3
  7. Shekarar 2007 - Kwanaki 90
  8. Shekarar 2009 - Kwanaki 8
  9. Shekarar 2009 - Kwanaki 120
  10. Shekarar 2010 - Kwanaki 157
  11. Shekarar 2011 - Kwanaki 59
  12. Shekarar 2013 - Kwanaki 165
  13. Shekarar 2017 - Kwanaki 35
  14. Shekarar 2018 - Kwanaki 94
  15. Shekarar 2020 -Kwanaki 120

Kara karanta wannan

Barazana ta sa Shugabannin ASUU sun canza wajen taron shirin shiga yajin-aiki

Bayan barazana da kai ruwa rana, a yau ASUU ta sake shiga yajin aiki, sai Allah yasan ranar dawowarsu.

A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki

A wani labarin, Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta ayyana shiga cikakken yajin aiki bayan tattaunawa mai zurfi, inji rahoton Punch.

An ayyana yajin aikin ne a wani taron manema labarai da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya hada, inda ya yi jawabi a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

Mambobin majalisar zartaswar kungiyar ta kasa sun gudanar da taruka kan batun yajin aikin tun ranar Asabar a jami’ar Legas mai taken, ‘NEC for NEC.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel