Barazana ta sa Shugabannin ASUU sun canza wajen taron shirin shiga yajin-aiki

Barazana ta sa Shugabannin ASUU sun canza wajen taron shirin shiga yajin-aiki

  • A daren yau ne ya kamata kungiyar ASUU ta cin ma matsaya a kan batun sake shiga wani yajin-aiki
  • Tun a ranar Asabar shugabannin ASUU su ke ta faman taron majalisar NEC a jami’ar UNILAG a Legas
  • Kwatsam sai aka ji an canza dakin da ake zama saboda zargin ana jin abinda ASUU ta ke tattaunawa

Lagos - Zaman kungiyar ASUU ta canza zani inda malaman jami’ar suka fasa yin taron da suka shirya a dakin taro na Ade Ajayi a jami’ar Legas.

Jaridar Daily Trust ta ce shugabannin ASUU sun maida taron na su na ranar Lahadi zuwa dakin laccar Tayo Aderinokun saboda zargin gwamnati.

Kungiyar malaman jami’ar ta na tsoron cewa jami’an gwamnatin Najeriya su na da labarin abin da ake yi a wurin da aka shirya za a yi zaman jiya.

Kara karanta wannan

ASUU za tayi zamanta na karshe yau, gobe za ta yanke shawara kan yajin aiki

Akwai yiwuwar gwamnati ta sa kayan leken asiri da za su sauraro mata abin da ASUU take tattaunawa, don haka aka canza inda za a shirya taron.

Rahoton ya ce a ranar Lahadi, 13 ga ga watan Fubrairu da kimanin karfe 12:00 kungiyar ta shiga taron da za ta dauki mataki a kan shiga yajin-aikin.

Premium Times ta ce tun ranar Asabar ake yin wannan taro da malaman jami’ar tayi wa take da “NEC for NEC” domin a san matakin da za a dauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan ASUU
Shugabannin ASUU a taro Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

Abin da ya faru - 'Dan ASUU

Wani jagora na kungiyar ta ASUU ya shaidawa manema labarai abin da suke tunanin ya faru.

“Kun san halin da ake ciki, saboda haka dole ASUU ta yi taka-tsan-tsan sosai. Mun samu labari cewa ana samun labarin abin da muke tattaunawa cikin dare.”

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta dage taron gangamin ta a shiyyar Arewa maso Yamma

“A dalilin haka dole mu ka sauya wajen taron domin cigaba da yin zama ranar Lahadi. Muhimmin lamari ne wannan, a daren yau za mu cin ma matsaya.”

Dakin laccar Tayo Aderinokun yana kusa da gidajen ajiye baki na musamman a jami’ar ta UNILAG.

Idan mun tafi shi kenan - ASUU

Ku na da labari cewa kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta reshen Owerri, tayi barazanar garkame jami’o’i sai lokacin da Allah ya yi, idan suka sake shiga yajin aikin.

An ji kungiyar ta ASUU ta na cewa ba za ta bude makarantu ba har sai an cika masu duka alkawuran da gwamnati tayi masu kafin su koma bakin aiki a 2020.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa mafi yawan malaman jami’a su na goyon bayan a tafi yajin-aikin da babu ranar dawowa saboda an gagara cika masu tulin alkawura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel