A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki

A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki

  • ASUU ta sanar da tsunduma yajin aiki bayan da kungiyar ta zauna zaman tattaunawa kan samar da maslaha
  • Ya zuwa yanzu, gwamnati ta gagara cika alkawuran da ta dauka tsakaninta da ASUU, lamarin da bai yiwa kungiyar dadi ba
  • Kungiyar ta sanar da dalibai da iyaye da daukacin al'umma abin da ke tsakaninta da gwamnatin Najeriya

Najeriya - Kungiyar malaman jami'a wato ASUU ta ayyana shigarta cikakken yajin aiki bayan tattaunawa mai zurfi da hukumomin zartasrwata, inji rahoton Punch.

Ta ayyana wannan yajin aikin ne a wani taron manema labarai da shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ya hada, inda ya yi jawabi dalla-dalla kan batun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

Kungiyar malaman Jami'a ta ASUU ta shiga yaji
A hukumance: Daga karshe ASUU ta tsunduma yajin aiki, ta fadi kwanakin da za ta yi | Hoto: thyenationonlineng.net
Asali: UGC

Mambobin majalisar zartaswar kungiyar ta kasa sun gudanar da taruka kan batun yajin aikin tun ranar Asabar a jami’ar Legas mai taken, ‘NEC for NEC.'

Kara karanta wannan

1999 zuwa 2022: Jerin lokutan da ASUU ta shiga yajin aiki, da adadin kwanakin da ta yi

ASUU ta wayar da kan malamai da dalibai a dukkan jami’o’i kan dalilin da ya sa kungiyar ta shirya yajin aikin.

Osodeke ya bayyana cewa, yajin aikin na tsawon makwanni hudu ne a duk fadin kasar, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

“Majalisar zartaswa ta kasa ta kungiyarmu ta kuduri aniyar fara yajin aiki na tsawon makonni hudu daga ranar 14 ga watan Fabrairu."

Tushen batun

Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta kan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika wasu alkawurran da ta kulla tun a shekarar 2009.

A ranar 15 ga Nuwamba, 2021, ASUU ta ba gwamnatin tarayya wa’adin makonni uku domin gaggauta biya musu bukatunsu.

Malaman sun yi barazanar sake komawa yajin aikin sakamakon zargin "rashin alkawari da gwamnati ta nuna" wajen aiwatar da yarjejeniyar da ta shiga da kungiyar, wanda ya kai ga dakatar da yajin aikin a 2020.

Kara karanta wannan

Za a kara laftawa Gwamnatin Buhari ciwon kai, Kungiyar NUPENG na shirin yajin-aiki

Bayan taron ASSU a Jami’ar Abuja a ranakun 13 da 14 ga watan Nuwamba, Shugaban ASUU, ya koka da cewa duk da ganawar da ya yi da Ministan Kwadago da Aiki, Dakta Chris Ngige, a ranar 14 ga Oktoba, 2021, kan batutuwan da kungiyar ke bore akai, gwamnati ta yi shuru.

Bayan wannan barazanar, karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, ya yi alkawarin cewa za a biyawa kungiyar bukatunta.

Makonni kadan, ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi, domin an biya malaman jami’o’in tarayya alawus na Naira biliyan 22.1.

Shugaba Buhari ya gana da shugabanni, ciki har da na addinai kan lamarin da ya shafi yarjejeniyar gwamnati da ASUU ta 2009.

ASUU tace Pantami bai cancanci zama Farfesa ba, zata hukunta FUTO

A wani labarin, kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda

Punch ta rahoto cewa ƙungiyar bayan taron mambobin majalisar zartarwan ta da ya gudana yau, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, "karan tsaye ga doka."

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa, Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel