Babban magana: Gwamnan PDP ya yi ikirarin cewa ‘mayu’ sun maka gwamnatinsa a kotu

Babban magana: Gwamnan PDP ya yi ikirarin cewa ‘mayu’ sun maka gwamnatinsa a kotu

  • Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa mayu sun maka gwamnatin jihar a gaban kotu
  • Udom ya ce sun maka shi kotu ne saboda aikin gina wajen bautar Allah na biliyoyin naira da ake yi, wanda su a ganin su hakan ba daidai bane
  • Ya ce sun yi nasara a kan mutanen amma kuma sai suka sake daukaka kara

Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya bayyana cewa mayu sun maka gwamnatin jihar a gaban kotu saboda gina cibiyar bauta ta kirista a jihar, Premium Times ta rahoto.

Mutane da dama sun soki gina wajen bautar na biliyoyin naira wanda ke gudana a yanzu haka a Uyo, inda suke ganin kamata ya yi da an yi amfani da kudin wajen magance muhimman abubuwan ci gaba a jihar mai arzikin man fetur.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Sai dai kuma, Mista Emmanuel ya sha yin jayayya cewa akwai bukatar gina wajen bautar Allah a Akwa Ibom a matsayinta na jaha da aka sanya ma sunan Allah.

Babban magana: Gwamna ya yi ikirarin cewa ‘mayu’ sun maka gwamnatinsa a kotu
Babban magana: Gwamna ya yi ikirarin cewa ‘mayu’ sun maka gwamnatinsa a kotu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wani shirin kai tsaye da aka watsa a gidan radiyo da talbijin a ranar Asabar, an jiyo gwamnan yana cewa:

“Dukka mayu sun hadu sun kai ni kotu cewa muna gina wajen bauta na Kirista.”
“Sun ce su basu yarda da Allah ba. Shari’ar tana nan a kotu, mun yi nasara a kansu amma sun daukaka kara.”

Emmanuel wanda ya zabi daya daga cikin yan majalisarsa a matsayin wanda zai gaje shi a zaben 2023, yana amsa tambayan manema labarai ne kan ko da gaske Allah ya nuna masa magajinsa kamar yadda ya yi ikirari.

Kara karanta wannan

Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

Yayin da yake amsa tambayar, sai ya magantu kan yadda “mayu” suka maka shi da gwamnati a gaban kotu.

Maganar mayu da gwamnan ya yi shi ya fi daukar hankali cikin batutuwan da ya fadi game da gwamnatinsa, inda mutane da dama daga jihar suka yi sharhi kan hakan a soshiyal midiya.

Don haka, daya daga cikin hadiman gwamnan, Aniekeme Finbarr, ya gaggauta zuwa Facebook domin yin Karin haske game da furucin gwamnan.

Mista Finbarr ya ce gwamnan na magana ne kan wata kara da kungiyar wadanda basu yarda da Allah ba ta Najeriya ta shigar kan gwamnatin Akwa Ibom a 2019 domin a hana gwamnatin gina wajen bauta.

Kotun ta yi watsi da shari’ar sannan ta ci tarar kungiyar N500,000.

Mista Finbarr ya ce:

“Zai baka dari amma da gaske ne. An yi yunkurin dakatar da aikin ginin ta hanyar amfani da doka.”

Gwamnan PDP ya bayyana sunan wanda zai gaji kujerarsa a 2023

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

A wani labarin, gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya ayyana kwamishinan ƙasa da albarkatun ruwa, Umo Eno, a matsayin wanda yake so ya gaje kujerarsa a 2023.

The Nation ta rahoto cewa zaɓin gwamnan ya haddasa rarrabuwar kai a majalisar zartarwa da kuma jam'iyyar PDP reshen jihar, inda mambobi da dama su kai watsi da lamarin.

Gwamna Emmanuel ya faɗi matsayarsa ne ranar Lahadi da daddare a wurin wani taro da ya ƙunshi shugabannni a jihar da kuma masu hanƙoron kujerar gwamna, cikin su harda yan majalisu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel