Sabon Nishadi: AREWA24 ta samar da sabon fannin shirya fina-finai masu kayatarwa

Sabon Nishadi: AREWA24 ta samar da sabon fannin shirya fina-finai masu kayatarwa

  • Tashar samar da fina-finai da sauran shirye-shirye ta AREWA24 na shirin samar da wani sabon fannin samar da fina-finai
  • Tashar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda tace fannin zai samar da shirye-shirye masu kayatarwa
  • A baya, gidan talabijin na AREWA24 dai ya samar da fina-finai masu dogon zango, wadanda suka shhara a Najeriya

Najeriya - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, tashar talabijin da shirye-shirye cikin harshen Hausa ta AREWA24 ta sanar da samar da sabon fannin samar da shirye-shiryen wasan kwaikwayo da fina-finai a shekarar nan ta 2022.

Sanarwar da aka fitar ranar Lahadi ta ce tashar za ta tsara, ta rubuta, ta kuma samar da wasu sabbin shirye-shiryen wasan kwaikwayo da ke ba da labarin ingantattun abubuwan Afirka daga Arewacin Najeriya da Afirka ta Yamma a cikin harshen Hausa da turanci.

Kara karanta wannan

Ango ya barke da kuka wajen bikin aurensu saboda tuna mutuncin da Amarya tayi masa

AREWA24 za ta samar da sabon shiri
Sabon nishadi: AREWA24 ta fara aikin wani sabon shiri mai dauke da nishadin gaske | Hoto: dailyrust.com
Asali: UGC

AREWA24 sun riga sun shirya da kuma watsa shirye-shiryen wasan kwaikwayo da suka fi shahara kuma mafi inganci a Arewacin Najeriya da Afirka ta Yamma, wato 'Dadin Kowa' da 'Kwana Casa'in' (90) kafin sanar da samar da sabon fannin.

Sanarwar ta kara da cewa ana kan aikin samar da sabon fannin shirya shirye-shiryen wasannin kwaikwayon a halin yanzu kuma kamfanin zai fara haska fim dinsa na farko daga fannin a zango hudu na 2022.

Ya aikin AREWA24 yake a bangaren shirya fina-finai?

A cewar Jacob Arback, shugaban AREWA24:

"AREWA24 ta fara bunkasa wasu fitattun marubuta, furodusoshi, daraktoci, editoci, da 'yan wasan kwaikwayo na Najeriya tun bayan kaddamar da tashar shekaru takwas da suka wuce.
“Yanzu mun zama manyan masu shirya ingantattun shirye-shiryen da suka shafi Afirka ga 'yan Najeriya, Afirka, da kuma masu kallo a Yammacin duniya wadanda ke kara kaunar labarai na musamman da jan hankali da ake ba da su a cikin wasannin kwaikwayo masu inganci da kuma fina-finai daga nahiyar."

Kara karanta wannan

'Yar Bokon gaske: Yadda matashiya ta kame kanta, ta kammala digiri da CGPA 7.0

Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro Arback na cewa:

“Manufarmu ba wai kawai mu kirkiro wasannin kwaikwayo masu shahara da cin nasara ga mabiyanmu Hausa bane.
"Wasu daga cikin abubuwan da muke shiryawa ba lallai su fara fitowa a AREWA24 ba. A nan gaba, muna shirin kirkirar jerin shirye-shiryen da kan iya jan hankalin masu kallo a duk fadin Afirka da sauran kasashen duniya."

Bayan dogon jira, fim din 'Gidan Badamasi' zango na 4 zai shiga kasuwa nan kusa

A wani labarin, shirin wasan barkwanci na Gidan Badamasi zango na 4, wanda ake jira shine zai zai shigo kasiwa a ranar 6 ga Janairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Malam Falalu Dorayi, wanda shi ne ya shirya shirin, ya ce zango na 4 zai fi armashi fiye da na baya domin an sake samo sabbin taurari masu barkwanci da karin kwararrun ma’aikata fiye da da.

Kara karanta wannan

'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara

Falalu ya kuma bayyana cewa an dauki shirin a wurare daban-daban a jihar Kaduna kuma an cusa wasu sabbin sassa masu ban sha'awa a cikin shirin domin kayatar da masu kallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel