'Yar Bokon gaske: Yadda matashiya ta kame kanta, ta kammala digiri da CGPA 7.0

'Yar Bokon gaske: Yadda matashiya ta kame kanta, ta kammala digiri da CGPA 7.0

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya, Cynthia Okafor, ta sha yabo a yanar gizo bayan da ta zama fitacciyar daliba a fannin Pharmacy tare da maki mai kyau
  • Budurwar ta sami damar samun CGPA 6.9, wanda ya sa ta zama mafi kwazo a cikin wasu 19 da suka kammala da CGPA 6.0
  • Cynthia ta godewa Allah da ya taimake ta fiye da kokarinta yayin da ta wallafa hotunan kammala digirinta a shafin Twitter

Ibadan, Oyo - Wata budurwa mai suna Cynthia Okafor Chidera, ta tafi shafin Twitter domin murnar nasarar da ta samu a fannin karatu bayan da ta zama daliba mafi kwazo da ta samu digiri a fannin hada magunguna (Pharmacy) a jami’ar Ibadan (UI).

Don cimma wannan babban burin, dalibar ta UI ta sami CGPAn da ya kai 6.9 daga 7.0. Cynthia wacce ta yada hotunan lambar yabo da ta samu bayan kammala karatun ta a yanar gizo ta ce Allah ne ya taimake ta ta samu nasarar.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Ta gama digiri da maki mai kyau
Abin da ba a taba ba: Matashiya ta tsara rayuwarta, ta kammala digiri da CGPA 7.0 | Tushen hoto: @cynthiaokafor
Asali: Twitter

Nasara daga Allah

Ta yarda Allah ne ya bata nasara bayan kokarinta na dan adam. An ga ‘yan Najeriya da dama a sashin sharhinta na Twitter suna taya ta murna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin rubuta wannan rahoto, faifan bidiyon ya tattara dangwake fiye da 12,000 tare da daruruwan sharhi daga mutane.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@BENDON43 ya ce:

"Ina matukar taya ki babban murna... Ina matukar alfaharin cewa ina tayaki murna, daga karkashin kasan zuciyata."

@AndersonOvuakp1 ya ce:

"Ina taya kimurna!!!"

@kizymoo ya ce:

"INA TAYA KI MURNA!"

@zibiduba said:

"Allah ya datar da ke, ina taya ki murna."

@sir_oluwasegun said:

"Ban taba ganin wani mara tsoro ba, kuma cike da juriya irin na wannan matar. Zan kira ta 2 na safe, 11 na dare, 1 na dare, 6 na yamma, 4 na yamma kullum tana nan. Na gode Cynthia."

Kara karanta wannan

Wani Saurayi ya lakadawa budurwarsa duka har ta mutu bayan ya dirka mata ciki

@9 ya ce:

"Pharmacy na amfani da 7.0 cgpa ne? Wow."

@BluvDt ya ce:

"Ina taya ki murna. Ba za a barmu a baya ba."

Barka: Ministan Najeriya da ya tafi karo ilmi ya kammala Digir-gir a Jami’ar Birtaniya

A wani labarin, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter a watan Maris a 2021, Hadi Sirika ya kare kundin binciken da ya rubuta a gaban malaman jami’a.

Hadi Sirika yana karatun digiri na M.Sc a jami’ar City University da ke Landan, kasar Ingila.

Paul Clark shi ne malamin da ya duba binciken da Ministan Najeriyar ya yi a kan samun hadin-kai tsakanin kasashen Afrika a harkar kula da jiragen sama.

Taken Nazari da binciken da Sirika ya yi shi ne "The development of Airline traffic in Nigeria and the relevance of single African Air transport market (SAATM).”

Asali: Legit.ng

Online view pixel