Sokoto: Iyalan Ma'aikacin gwamnati da aka kama da hannu a ayyukan yan bindiga sun yi magana

Sokoto: Iyalan Ma'aikacin gwamnati da aka kama da hannu a ayyukan yan bindiga sun yi magana

  • Ma'aikacin gwamnatin jihar Sokoto, Ladan Ibrahim, na ɗaya daga cikin mutum 45 da aka damƙe kan zargin taimakawa Boko Haram da kuɗaɗe
  • Iyalan Malam Ibrahim sun bayyana halin da suka tsinci kan su tun bayan kama jigon da yake ɗaukar nauyin su baki ɗaya
  • Amaryarsa, Habiba Ladan Ibrahim, ta ce abin da za su ci a rana wataran gagarar su yake, balle a yi maganar lafiya da makarantar yara

Sokoto - Iyalan ma'aikacin gwamnati a Sokoto, Ladan Ibrahim, wanda aka kama da zargin hannu a rura wutar ta'addanci da kuɗi sun yi kira ga hukumomi su gaggauta bincike kan lamarin.

Ɗaya daga cikin iyalan Ibrahim wanda ya zanta da wakilin daily trust ta wayar Salula, yace sun shiga halin ƙaƙanikayi tun bayan kama shi.

A cewarsa tun bayan gayyatar da aka masa kuma aka tsare shi, rayuwarsu ta canza, domin shi kaɗai ke ɗaukar nauyin kula da su da kuma yan uwansa.

Taswirar jahar Sokoto
Sokoto: Iyalan Ma'aikacin gwamnati da aka kama da hannu a ayyukan yan bindiga sun yi magana Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mambobin iyalan Ladan Ibrahim sun haɗa da mata hudu da kuma ƴaƴan da suka haifa masa guda 16.

Da take magana a madadin sauran mambobin Iyalan Ibrahim, ɗaya daga cikin matansa, Habiba Ibrahim Ladan, ta ce matsananciyar rayuwar da suka shiga ta kai maƙura.

Matar ta ce:

"Ni ce matarsa ta huɗu (Amarya) kuma ina magana ne a madadin sauran yan uwan na, A'i, Fatima, da Uwani Ladan Ibrahim, da kuma yayan mu 16 da ma sauran yan uwansa baki ɗaya."
"Mun shiga matsananciyar rayuwa tun da ya bar mu. Da ni da Uwar gidansa ba mu cikin koshin lafiya, ina zuwa Asibiti duk wata, ita kuma tana zuwa duk mako, amma tun da aka kama shi dole muka daina zuwa."
"Yayan mu sun daina zuwa makaranta, abin da zamu ci gagaran mu yake. Shi ne jagora a cikin mu wanda yake tallafa mana da yan uwansa, wallahi muna shan wahala."

Habiba ta kara da rokon cewa gwamnati ta taimaka ta gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhumar da ake masa, aƙalla ran mu zai yi sanyi ganin an masa adalci.

Waye Ladan Ibrahim?

Ladan Ibrahim ya yi aiki a hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, yanzu kuma ya koma ma'aikatar ilimin gaba da sakandire ta jihar Sokoto.

Yana ɗaya daga cikin mutum 45 da aka kama da zargin hannu a ayyukan ta'addanci mai alaƙa da kungiyar Boko Haram.

Rahoto ya nuna cewa yanzu haka yana tsare a hannun jami'an hukumar tsaron fasaha Defence Intelligence Agency a Abuja.

A wani labarin na daban kuma Ɗalibar 200-Level a Jami'ar Najeriya ta faɗa cikin Masai, Allah ya mata rasuwa

Wata ɗaliba a jami'ar Obafemi Awolowo dake shekara ta biyu a karatu, Ajibola Ayomikun, ta faɗa cikin shadda kuma ta mutu.

Mai magana da yawun jami'ar OAU, Abiodun Olarewaju, yace an yi kokarin kai mata agaji, amma ana isa Asibiti rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel