Nasara: Jiragen yakin Najeriya sun yi ruwan wuta kan kwamandojin yan bindiga a jihar Neja

Nasara: Jiragen yakin Najeriya sun yi ruwan wuta kan kwamandojin yan bindiga a jihar Neja

  • Bayan yanayi ya gyaru a sama, jiragen yakin rundunar sojin Najeriya sun yi luguden wuta kan yan bindiga a jihar Neja
  • Rahoto ya nuna cewa Dakarun sojin ƙasa sun marawa jiragen baya har aka kashe jagororin yan bindiga da yaransu 37
  • Wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin da idonsa, yace sun ga yan bindiga da bakaken kaya na neman tsira da ransu

Niger - Wasu jiragen yaƙin rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar kashe Kwamandojin yan bindiga da yawan gaske a wani samame da suka kai maɓoyar su a jihar Neja.

BBC Hausa ta rahoto cewa yan ta'addan sun matsawa al'umma da kai munanan hare-hare yankunan kananan hukumomi uku da suka haɗa da Rijau, Mariga da Kontagora a jihar.

Kara karanta wannan

An yi jana'izar DPOn yan sandan da yan bindiga suka kashe a Jibia

Maharan sun kone gidajen mutane, sun kwashe kayayyaki masu yawan gaske a shaguna, sun kashe yara ƙananan, kuma suka sace dandazon dabbobi.

Jirgin Helikwafta
Nasara: Jiragen yakin Najeriya sun yi ruwan wuta kan kwamandojin yan bindiga a jihar Neja Hoto: prnigerian.com
Asali: UGC

Wani babban jami'i a rundunar sojin Najeriya ya shaida wa jaridar PRNigeria cewa yanayin hazo mara kyau ne ya hana jiragen yaki su kaddamar da hari kan yan bindigan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai daga baya, bayan samun kyaun hanya, Rundunar soji ta aika jirgin yaƙin Alpha da kuma wani Helikwafta domin su kai hari ta sama kan yan bindigan.

Bugu da kari, Dakarun sojin ƙasa na Najeriya suka mara wa jiragen baya ta ƙasa, inda aka yi wa yan ta'addan ruwan wuta ta sama da ƙasa.

Yan bindiga nawa sojoji suka kashe?

Wani shaidan da ya gane ma idonsa, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce sun ga yan bindiga sanye da baƙaƙaen kaya na gudun neman tsira da rayukan su.

Kara karanta wannan

Yan bindigan sanye da kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa har lahira

A cewar mutumin, bayan jiragen yaƙin sun gama luguden wuta, "an ga yan bindigan na gudun tsira, kuma sun tsere sun bar gawarwakin waɗan da aka kashe."

Ɗaya daga cikkn Jami'an kungiyar Sa'kai ya bayyana cewa:

"Mun ƙidaya gawarwakin yan ta'adda 37 da suka mutu sanadin harin, cikin su har da waɗan da muke tsammanin shugabannin su ne."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari, sun kashe fitattun Shugabanni 7 a jihar Imo

Aƙalla shugabannin al'umma bakwai yan bindiga suka kashe a yankin Mmahu dake ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema, jihar Imo .

The Cable ta rahoto cewa yan bindiga sun halaka sanannun shugabannin mutane ne yayin da suka farmaki ƙauyen da safiyar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel