Gaba ta kai ni: Bayan barın PDP zuwa APC, Sanata ya tashi da babban matsayi a majalisar dattawa

Gaba ta kai ni: Bayan barın PDP zuwa APC, Sanata ya tashi da babban matsayi a majalisar dattawa

  • An nada Emmanuel Bwacha daga jihar Taraba a matsayin shugaban kwamitin sayan kayayyaki na majalisar dattawa
  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya nada shi a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu
  • Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan sanatan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya nada tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, a matsayin shugaban kwamitin sayan kayayyaki na majalisar dattawa.

An sanar da nadin Bwacha ne a zauren majalisar a yau Laraba, 9 ga watan Fabrairu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Gaba ta kai ni: Bayan barın PDP zuwa APC, Sanata ya tashi da babban matsayi a majalisar dattawa
Bwacha ya zama shugaban kwamitin sayan kayayyaki na majalisar dattawa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

A makon da ya gabata ne, dan majalisar ya sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Hakazalika, shugaban majalisar dattawan ya sanar da sabon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar, Sanata Shuaibu Isa Lau a matsayin sabon mataimakin shugaban kwamitin ayyuka na majalisar, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya sauya sheka zuwa APC

A baya mun kawo cewa Sanata mai wakiltan Taraba ta kudu kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi Bwacha zuwa APC a hukumance a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu, inda ya mika masa tutar jam'iyyar mai mulki.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya gabatarwa Buhari da Bwacha a fadar Villa da ke Abuja.

Guguwar sauya sheka: Ana gab da yiwa APC mai kankat gabannin 2023 - Tambuwal

A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tabbacin cewa kwanan nan za ta tarbi masu sauya sheka daga sauran jam’iyyun siyasa gabannin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: PDP ta naɗa sabon mataimakin marasa rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, yayin ziyararsa ta uku kan neman shawara game da kudirinsa na neman tikitin shugaban kasa na PDP a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel