Da Dumi-Dumi: PDP ta naɗa sabon nataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa

Da Dumi-Dumi: PDP ta naɗa sabon nataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa

  • Jam'iyyar hamayya PDP mai marasa rinjaye ta naɗa sabon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Najeriya
  • A wasikar da Sanata Ahmad Lawan ya karanta yau, PDP ta naɗa Sanata Shuaibu Lau, a matsayin wanda zai maye gurbin Sanata Bwacha
  • Hakan ta faru ne biyo bayan sauya shekar tsohon mai rike da kujerar, Sanata Emmanuel Bwacha zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Abuja - Jam'iyyar PDP mara rinjaye ta naɗa Sanata Shu'aibu Lau, (Taraba ta arewa) a matsayin sabon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya.

The Nation ta rahoto cewa kujerar ta zama babu kowa biyo bayan sauya shekar mai rike da ita a baya, Sanata Emmanuel Bwacha (Taraba ta Kudu) zuwa APC a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP dake neman gaje Buhari ya dira Zamfara, ya gana da mataimakin Gwamna

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawal, shi ne ya karanta wasikar naɗin daga shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.

majalisar dattawa
Da Dumi-Dumi: PDP ta naɗa sabon nataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Lawan ya bayyana Sanata Bwacha a matsayin sabon mamban jam'iyyar APC a hukumance a zaman majalisar na yau Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban majalisa ya umarci Sanata Orji Kalu ya kai Bwacha sabuwar kujerarsa a sashin da aka ware wa mambobin jam'iyya mai mulki.

Sanata Kalu ya cika umarnin shugaban majalisa duk da watsin da mambobin PDP marasa rinjaye suka yi da cigaban, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Mambobin PDP ba su amince da sauya shekar ba

Sanata George Sekibo na jam'iyyar PDP ya yi yunƙurin jan hankalin majalisa kan karya doka wajen sauya sheƙar Sanata Bwacha, amma ya gamu da cikas.

Shugaban majalisar ya dakatar da shi tare da kafa masa hujja da wasikar maye gurbin Sanata Bwacha da shugaban PDP na ƙasa ya aiko zauren majalisa.

Kara karanta wannan

Buhari ya nufo gida Najeriya bayan kammala taron kungiyar gamayyar kasashen Afrika

Bisa wannan cigaban, Sanata Lawan ya bayyana cewa APC mai mulki na da Sanatoci 70, yayin da PDP ke da 38, sai kuma jam'iyyar YPP dake da mutum ɗaya.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe kujerun ciyamomi 21 da kansiloli 225 a jihar Kebbi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi da ya gudana ranar Asabar.

Shugaban hukumar KESIEC, Aliyu Muhammad Mera, yace jam'iyyar APC ta lashe baki ɗaya kujerun Ciyamomin jihar da Kansiloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel