Rikici kan sanya Hijabi a Kwara: MURIC ta fusata, ta zargi 'yan sanda da sanya wajen bincike

Rikici kan sanya Hijabi a Kwara: MURIC ta fusata, ta zargi 'yan sanda da sanya wajen bincike

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta zargi hukumar yan sanda da yin sanya wajen bincike kan batun kisan wani dalibi a yayin zanga-zanga kan sanya hijabi a makarantar Baptist
  • Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya nuna takaici matuka game da halin rashin kishin da ‘yan sanda ke nunawa a kan lamarin
  • An dai tattaro cewa wasu yan daba ne suka farma daliban da ke zanga-zanga kan batun sanya hijabi zuwa makaranta, inda suka harbe wani dalibi Habeeb Idris har lahira

Kwara - Daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), Farfesa Ishaq Akintola, ya zargi rundunar yan sanda da yin sanya kan batun kisan wani dalibi, Habeeb Idris, na makarantar Baptist, Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara.

Kara karanta wannan

'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara

An tattaro cewa an harbe dalibin ne a ranar Alhamis, a yayin gudanar da zanga-zanga kan hijabi. An kuma ce wasu dalibai hudu sun jikkata a lamarin.

Akintola ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Rikici kan sanya Hijabi a Kwara: MURIC ta fusata, ta zargi 'yan sanda da sanya wajen bincike
Rikici kan sanya Hijabi a Kwara: MURIC ta fusata, ta zargi 'yan sanda da sanya wajen bincike Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Vanguard ta nakalto yana cewa:

“Daya daga cikin dalibai hudu da suka jikkata a yayin zanga-zanga kan sanya hijabi a makarantar Baptist, Ijagbo a karamar hukumar Oyun da ke jihar Kwara, ya rasu. Dalibin wanda ya kasance musulmi mai shekaru 20, Habeeb Idris, ya jikkata sosai sakamakon harbin bindiga a ranar 3 ga watan Fabrairun 2022.
“Wasu dalibai uku sun ji rauni daban-daban sakamakon mummunan harin da wasu yan daba wadanda suka dage cewa babu musulmar da za a bari ta yi amfani da hijabi a makarantar suka kai.

Kara karanta wannan

Hana sa Hijabi a Kwara: Ba zamu lamunci wannan rainin hankalin ba: Kungiyar Musulmai

“Amma kokarin da ake yi na ganin yan sandan jihar Kwara sun kamo maharan ya ci tura. Koda dai daliban da suka ji rauni sun kasance a ofishin rundunar jiya don yin korafi da gano wadanda suka far masu, yan sandan basu nuna shirin bin su ba.
“Mun ji takaici matuka game da halin rashin kishin da ‘yan sanda ke nunawa a jihar Kwara. Me yasa ‘yan sanda ke samun sanya a kan wannan lamarin?’’

'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara

A gefe guda, ministan ilimi, Adamu Adamu, ya mayar da martani kan cece-kucen da ake tafkawa a baya-bayan nan kan yadda ake tauye hakkin mata musulmi da ke sanya hijabi a wasu sannan kasar.

Adamu ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa mata musulmi cikakken daman sanya Hijabi daidai da koyarwar addininsu, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mutum 1 ya mutu, da dama sun jikkata yayinda aka kaiwa Musulmai masu zanga-zanga kan hijabi hari

Ya bayyana hakan ne a wajen taron jama’a da kungiyar hadin kan mata musulmi ta Najeriya ta shirya a wani bangare na gudanar da bikin ranar Hijabi ta duniya na bana a ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu a babban masallacin kasa dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel