Zargin hannu a Boko Haram: Tun 2011 ake bincike na, Ali Modu Sheriff

Zargin hannu a Boko Haram: Tun 2011 ake bincike na, Ali Modu Sheriff

  • Tsohon gwamnan Borno Ali-Modu Sheriff ya musanta zargin sa da ake da hannu a Boko Haram,a cewar sa jami'an tsaro sun dade suna binciken sa tun saukar sa daga mulki
  • Shugaban kungiyar kanfen din sa, Victor Lar ya musanta hakan ne yayin tattauna wa a ranar Lahadi da NAN a Abuja.
  • Victor Lar ya buga kirji ya ce duk wanda ke da wata alama da za ta gasgata ikirarin hakan ya fito ya fallasa

Tsohon gwamnan jihar Borno Ali-Modu Sheriff, ya musanta zargin sa da ake da hannu a Boko Haram, inda a cewar sa jami'an tsaron sun dade suna binciken sa tun bayan saukar sa daga mulki a shekarar 2011.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Shugaban kungiyar kamfen na Ali-Modu Sheriff, Victor Lar, ya musanta hakan ne yayin wata tattauna wa da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno

Zargin hannu a Boko Haram: Tun 2011 ake bincike na, Ali Modu Sheriff
Zargin hannu a Boko Haram: Tun 2011 ake bincike na, Ali Modu Sheriff. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya ce a matsayin Sheriff sanannan dan jam'iyyar APC, dan takarar shugaban jam'iyyar, wanda ya yi gwamnan Borno sau biyu kuma tsohon sanata, babu wani abu da ke tsakanin shi da 'yan Boko Haram.

"Sunan Sheriff baya daga cikin sunayen masu daukan nauyin yan Boko Haram kamar yadda hadaddiyar daular larabawa ta bayyana (UAE). Jami'an tsaron sun dade suna bincikar sa tun bayan saukar sa daga mulki a shekarar 2011, kuma ba su same sa da laifin da ake zargin sa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da akwai hannun shi a ciki, da tuni an damko shi ko kuma a fallasa shi duniya ta sa ni. Saboda haka, na bugi kirji na ce duk wanda ke da wata alama da za ta tabbatar da hakan ya fito ya bayyana," ya kara da hakan.

Kara karanta wannan

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

Lar ya ce maganar takarar Sheriff a matsayin shugaban jam'iyyar APC da ake cewa tana kasa tana dabo saboda EFCC na tuhumar sa, ba gaskiya bane, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

"Idan EFCC na tuhumar ka hakan na nufin ko dai an gurfanar da kai gaban kotu ko kuma an yanke maka hukunci. Babu mai tuhumar Sheriff. Idan kuna shakka a kan hakan, ku je EFCC ku bincika," a cewar Lar.

Da haka ne ya musanta zargin, inda ya ce jita-jita ne da labaran kanzon kurege kawai da wasu ke yadawa.

Ya tsaya a kan bakar sa na cewa, babu wanda ya taba kai Sheriff kotu ko kuma shi ya kai PDP kotu, tun lokacin da yake shugabancin jam'iyyar PDP kamar yadda ake yada wa.

Lar ya bayyana cewa sheriff ba shi bane wanda ya kai kara, sai dai shi ne wanda ake kare wa a matsayin sa na shugaban jam'iyyar PDP, inda ya sha alwashin idan ya zama shugaban jam'iyyar APC na kasa, babu wani abu mai kama da gurfanar wa.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

"Ina tabbatar muku, babu wanda za a gurfanar. Idan akwai, tabbas yawan zai ragu saboda za mu zamo masu sulhu," a cewarsa.

Lar, yayin hasashe game da taron jam'iyyar da zai gudana a 26 ga watan Fabrairu, ya ce akwai bukatar jam'iyyar ta yi taron sulhu kafin taron.

Ali Modu Sheriff: Muna fatan APC ta rike madafun iko na tsawon shekara 50

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce jam'iyyar jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar dole ne su yi aiki tare da gina wa jam'iyyar gadar da za ta tabbatar da ita a madafun iko har nan da shekaru 50, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Sheriff, wanda yayi Sanata sau uku kuma mai neman kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa, ya ce dole ne masu ruwa da tsakin jam'iyyar su hada kai wurin tabbatar da jam'iyyar ba ta tashi aiki ba bayan kammalar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun sace mutane kusan 60 a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel