Ali Modu Sheriff: Muna fatan APC ta rike madafun iko na tsawon shekara 50

Ali Modu Sheriff: Muna fatan APC ta rike madafun iko na tsawon shekara 50

  • Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce APC za ta cigaba da mulki har nan da shekaru 50 masu zuwa
  • Dan siyasan da ya lashe zaben Sanata har sau uku, ya tabbatar da cewa akwai bukatar 'ya'yan jam'iyyar su hade kai
  • Dan takarar shugabancin jam'iyyar APC na kasa, ya ce ko bayan wa'adin mulkin shugaba Buhari ya cika a 2023, za su cigaba da rike madafun iko

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce jam'iyyar jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar dole ne su yi aiki tare da gina wa jam'iyyar gadar da za ta tabbatar da ita a madafun iko har nan da shekaru 50, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Sheriff, wanda yayi Sanata sau uku kuma mai neman kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa, ya ce dole ne masu ruwa da tsakin jam'iyyar su hada kai wurin tabbatar da jam'iyyar ba ta tashi aiki ba bayan kammalar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Read also

Rikicin PDP: An kori shugabar mata, tsohon minista da wasu jiga-jigai a PDP

Ali Modu Sheriff: Muna fatan APC ta rike madafun iko na tsawon shekara 50
Ali Modu Sheriff: Muna fatan APC ta rike madafun iko na tsawon shekara 50. Hoto daga dailytrust.com
Source: Facebook

Tsoffin gwamnoni da wasu jiga-jigan 'ya'yan APC sun fara neman hanya tare da neman darewa kujerar shugabancin jam'iyyar ana tsaka da cece-kuce kan yankin da za a bai wa, Daily Trust ta wallafa.

Sheriff, wanda ya ke ta neman shawarwarin masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnoni, sanatoci da iyayen jam'iyyar APC ya ce:

"A yau, a matsayin mu na jam'iyya shekaru shida kacal muka yi a gwamnati. Muna hango wa APC cigaba da mulki har nan da shekaru 50 masu zuwa.
"Buhari ne ya kawo mu nan kuma muna tunanin abinda za mu fuskanta bayan wa'adin mulkinsa ya cika a matsayin shugaban kasa. Mu dai 'ya'yan jam'iyyar APC ne za mu sanar da duniya cewa za mu iya samun yardarsu ko bayan ya kammala mulkinsa.

Read also

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

"Domin yin hakan, muna bukatar kowa. Muna son jama'ar da suka san tarihin jam'iyyar, inda muka nufa, wadanda suka san tarihin kasar nan, wanda ya samu gogewa a fannonin rayuwa kuma muna bukatar aiki tare a kasar nan.
"Yin hakan ba zuwa zai yi da sauki ba, akwai bukatar mu kara kaimi. A don haka na yadda cewa akwai matukar amfani in garzaya wurin dukkan shugabannin jam'iyyarmu, matasa, mata, kungiyoyi daban-daban domin in sanar musu cewa jam'iyyar mu za ta yi karkon shekaru 30, 40 ko 50 da izinin Ubangiji."

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da ISWAP suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

A wani labari na daban, a yammacin ranar Alhamis ne dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar dakile wani farmaki da 'yan ta'addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) suka kai sansanin soji da kuma wasu yankuna na jihohin Borno da Yobe.

Read also

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

PRNigeria ta gano cewa, dakarun dauke da manyan makamai sun bankado yunkurin harin da miyagun 'yan ta'addan suka kai Malam Fatori da ke jihar Borno.

'Yan ta'addan da suka bayyana a motocin yaki da babura, zakakuran dakarun sun fi karfinsu inda suka batar da wasu daga ciki yayin da wasu suka ja da baya tare da tserewa.

Source: Legit.ng

Online view pixel