Da Dumi-Dumi: Fusatattun Mutanen gari sun hallaka tawagar yan fashi da suka kai hari

Da Dumi-Dumi: Fusatattun Mutanen gari sun hallaka tawagar yan fashi da suka kai hari

  • Mutanen gari sun samu nasarar kama wasu yan fashi da makami da suka addabi yankin su, kuma ba su yi wata-wata ba wajen aika su lahira
  • Wani shaida ya bayyana cewa an kama mutum biyu daga cikin yan fashin yayin da suka shiga wani garejin gyaran mota a Legas
  • Wannan dai ba shine karon farko da kwatankwacin haka ke faruwa ba, musamman yanzun da tsaro ya lalace a Najeriya

Lagos - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mutum biyu daga cikin tawagar mutum uku ta yan fashi da makami sun haɗu da ajalinsu a hannun mutanen gari.

Rahoto ya nuna cewa mutane sun yi ram da yan fashi ne yayin da suka kai hari wani garejin gyaran mota dake kan babbar hanyar Badagry a jihar Legas, da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar nan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile mummunan harin yan bindiga a Zamfara

Mutanen gari
Da Dumi-Dumi: Fusatattun Mutanen gari sun hallaka tawagar yan fashi da suka kai hari Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wani shaidan gani da ido yace waɗan da ake zargin sun jima suna aikata ta'addanci a yankin Okoko, Igbolerin, Iyana da sauran wuraren dake kewaye.

A cewarsa, mutanen da suka tattaru sun yi wa yan fashin rubdugu har suka kashe su, kasancewar dama suna kwana da baƙin cikin takurawar da suka musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan ba shi ne karo na farko da mutane ke nuna fushin su kan yan fashi da makami ba, ko wasu yan ta'adda da suka adda be su.

A kwanakin baya, wasu matasa sun huce fushin su kan wasu da ake zargin yan fashi da makami ne a Eziama- Obaire kusa da Mgbabano junction dake karamar hukumar Nkwerre jihar Imo.

Wani shaida da abun ya faru a idonsa, yace yan fashin sun yi yunkurin satar Babur, amma rashin sa'a tasa ɗaya ya shiga hannun Yan Okada da matasa, suka sheke shi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Matasa 'yan 'Yahoo' sama da 40 sun yi wa wata unguwa kawanya a Abuja

A wani labarin kuma Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa da Kwankwaso kan Takara a 2023

Rahoto ya nuna cewa bangaren mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun tuntubi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin haɗa kai a takarar 2023.

Kwankwaso, tsohon gwamnan jahar Kano kuma tsohon ministan tsaro a Najeriya, a halin yanzun babban jigo ne a jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel