Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile mummunan harin yan bindiga a Zamfara

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile mummunan harin yan bindiga a Zamfara

  • Jami'an tsaro a Najeriya da kuma haɗin guiwar yan Bijilanti, sun fatattaki tawagar yan bindiga yayin da suka kai hari yankin Gusau
  • Wani mazaunin yankin Magami dake Gusau, ya bayyana yadda jami'an suka tilasta wa yan ta'addan guduwa daga kai hari
  • Rahoto ya nuna cewa yan bindiga sun jima suna yunkurin kai hari Magami dake karamar hukumar Gusau, amma ba su yi nasara ba

Zamfara - Jami'an tsaron Najeriya tare da taimakon yan Bijilanti sun samu nasarar ɗakile mummunan nufin kai hari na yan ta'adda a garin Magami, ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara.

Daily Trust ta tattaro cewa yan bindigan a kan dandazon Babura sun yi yunkurin shiga garin da yammacin Lahadin nan, amma jami'an tsaro suka fatattake su.

Wani Mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Babangida, yace mutane ba su yi wata-wata ba wajen sanar da jami'an tsaro, yayin da suka ji labarin zuwan yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mutanen gari sun fusata, sun aika yan bindiga biyu Lahira yayin da suka kai hari

Taswirar jahar Zamfara
Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile mummunan harin yan bindiga a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mutumin yace:

"Mutane sun koma gefe, wasu sun fara gudun neman tsira. Yan kasuwa sun garƙame shagunan su, sun koma gidajen su domin shirya wa da jiran ko ta kwana."
"Sun zo a Babura da yawan gaske, suka taru a kusa da Sabon Garin Dutsen Kura, wanda ke nisan kilomita 15 daga garin Magami."
"Yayin da mazauna suka ji burbushin abin da ke shirin aukuwa, sai suka yi gaggawar sanar da jami'an tsaron dake zaune a garin Magami."

Yadda aka yi gumurzu

Babangida ya kara da cewa bayan samun bayani, jami'an tsaro da kuma yan Bijilanti, sun shirya kan su a bayan gari, suka jira isowar yan ta'addan.

"Jami'an tsaro da Yan Bijilanti sun shirya kan su a filin Sallar Idi dake gabashin garin kuma bayan haka ba da jimawa ba yan ta'adda suka ƙariso."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Niger ta saka dokar hana fita a kananan hukumomi 2

"Sun yi gumurzu tsakanins su, amma bisa tilas yan bindigan suka gudu, sai da suka rabu biyu saannan kowane ɓangare ya yi takansa."

Tun a baya dai, yan ta'addan sun yi yunkuri lokuta daban-daban na kai hari garin Magami amma har yanzun Allah bai ba su nasara ba.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin rundunar yan anda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ci tura.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

Yan fashi da makami sun farmaki motar dake ɗakko kuɗi ta Banki, sun kwamushe makudan kuɗaɗe a jihar Delta.

Rahoto ya nuna cewa yan fashin sun fasa motar da harsasan bindiga, yayin da suka ɗibi kudi suka yi gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel