Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi

Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi

  • Wani dan Najeriya ya ba da matukar mamaki a wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a wajen neman aurensa
  • Mutumin ya ba mutane mamaki yayin da ya kaftawa budurwarsa mari a fuska, wanda hakan ya tilasta mata rike rigarsa
  • Yayin da kowa ke kokarin tambayar abin da ke faruwa a tsakanin su biyun, sai ya durkusa a kasa ya mika zoben neman aurenta

Najeriya - A wani bidiyon da ke nuna saurayi na neman auren budurwa, wani mutum ya mari budurwarsa a bainar jama'a, inda ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Watakila hakan wani sabon salon nuna soyayya ne na musamman, bidiyon da aka dauka a cikin wani gida ya nuna saurayin ya kaftawa budurwa mari a fuska a gaban sauran mutanen da ke wurin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

Saurayi ya mari budurwa
Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi | Hoto: Screengrabs from video shared by @gossipmilltv
Asali: Instagram

Budurwa ta so ramawa

Wannan matakin ya fusata budurwar, lamarin da ya kai ga ta nemi ta rama tare da rike rigarsa yayin da ta ke shirin kafta masa mari kamar yadda ya yi mata a bainar jama'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A nan take, mutumin da sauri ya durkusa kan gwiwa daya, ya fito da zobe yana neman auren budurwar.

Bayan ta fahimci cewa marin yana cikin dabarar neman auren, budurwar ta durkusa ta karbi tayin aurensa.

Masu kallo a harabar gidan sun shiga matukar mamaki da ganin wannan lamari da ba a saba gani ba.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

@ajigagodson ya ce:

"Haukar ta yi yawa! Idan da ita ta mare ka sai ka fasa koh. Babu wani abu wai shi marin soyayya."

@ormorewhomie ya ce:

"Ina fatan ta tuna ta rama marin kafin ta amince. Mari da sunan tambaya, mari da sunan amsa. Duk soyayya ne!"

Kara karanta wannan

Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa

@sekani_bliss ya ce:

"Allah ma yasani, sai na rama kafin na karbi zoben, wannan wane irin wasan banza ne..."

@aisha4dable__collections sun bayyana:

"Ya saita kwakwalwarta kafin ya nemi aurenta, don idan ta ce A'a' ta sake karbar wani mari."

A wani labarin daban, kararrawar bikin aure na kadawa wata baiwar Allah wacce saurayunta ya amince da bukatar aurenta. Budurwar ta cire tsoro ta yi abin da ya dace, inda ta ba saurayinta zoben alkawari.

A cikin wani bidiyon da @instablog9ja ya yada a Instagram, an ga budurwar ta durkusa a gaban saurayin. Nan take ya mika hannunsa na hagu don karbar zoben aurenta.

Budurwar ta mike, inda suka hade tare da sumbatar juna. Amma wannan lamari fa ya jawo hankali sosai a kafar Instgram, tare da mutane da yawa ba su yarda da hakan gaske ya faru ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel