Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa

Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa

  • Wani dattijo mai shekaru 70, Leo, wanda ke da hangen nesa ya shirya komai da za a bukata a yayin bikin mutuwarsa
  • Leo ya bayyana cewa ya zama dole ya yi hakan saboda tsoffi da ke mutuwa a kauyensa suna zama gagarumin nauyi ga mutanen kauyen nasa ta fuskacin kudi
  • Mutumin wanda ke da matan aure tara ya kuma siya lemuka, akwatin gawa da duk sauran abun bukata yayin binne sa

Wani dattijo mai shekaru 70, Leo, ya haka kabarinsa a yayin da yake shirye-shiryen mutuwarsa. Mutumin ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda talakawan garinsa na shiga halin matsi don binne mutanen da suka mutu a baya-bayan nan.

Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa
Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa Hoto: @afrimax_tv
Asali: Instagram

A wani bidiyo da Afrimax ta wallafa, mutumin ya bayyana cewa baya so ya zama jidali ga mutane bayan ya mutu.

Kara karanta wannan

Tsoron mutuwa: Yadda attajirai ke zuba kudi don samar da injin da zai sa su tabbata a duniya

An biya kudin komai da komai

Domin cimma wannan manufa, mutumin ya haka kabarinsa, ya shirya komai da za a yi amfani da shi a yayin bikin mutuwarsa.

Mutumin ya siya isassun lemuka da za a rabawa bakin da za su halarci bikin mutuwarsa. Ya kuma tanadi siminti da tubalin da za a kawata kabarin da shi.

Leo wanda ke da mata tara ya biya masu daukar gawar da za su dauke shi. Tun da ya kammala shirye-shiryen binne shi, mutumin na amfani da lokacinsa wajen bikin sauran ranakun da suka rage masa cikin koshin lafiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Ga martanin jama'a game da lamarin:

franca_onome ya ce:

"Mutum ne mai hikima. A Afrika ne kadai muke barwa yan uwanmu da ke juyayi nauyin bikin binnemu. Yan Afrika basa taba yin tanadin mutuwarsu. Suna son zuwa Aljannah amma basa son mutuwa. Mutuwa bashi ne duk sai mun biya mai zai hana ka saukakawa masoyanka ta hanyar yi da kanka."

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

kingmac_47 ya ce:

"Mutumin da ke hangen gaba."

art.bamtech ya ce:

"Rana ce da ke bukatar tunani."

Iyalin mamaci sun mayarwa Gwamnati kudin Albashin shekara 11 da ya karba ba ya zuwa aiki

A wani labarin, iyalin marigayi Baba-Aji Mamman sun bayyana cewa sun mayar da kudi N11 million asusun gwamnatin jihar Yobe saboda rashin zuwa aikin mahaifinsu lokacin da yake raye.

Marigayin ya kasance tsohon ma'aikacin hukumar samar da wutan lantarki a karkara na jihar Yobe.

A sanarwan da iyalinsa suka yi ranar Laraba kuma aka wallafa a jaridar Daily Trust, sun nemi gafarar al'ummar jihar da ma'aikatar da yayi aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel