Evans ya yi fallasa mai ban mamaki game da Abba Kyari da yaransa

Evans ya yi fallasa mai ban mamaki game da Abba Kyari da yaransa

  • Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans ya fallasa wasu manyan bayanai dangane da Abba Kyari
  • A cewar Evans, Kyari da yaran sa sun azabtar da shi a lokacin da ake tsaka da tuhumarsa akan laifin garkuwa da mutane
  • Ya musanta batun garkuwa da wani dan kasuwar, Sylvanus Ahamonu da amsar kudin fansa daga hannun iyalansa na $420,000

Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans, a ranar Juma’a, 4 ga watan Fabrairu wanda ake zargin sa da garkuwa da mutane ya sanar da kotun laifuka na musamman ta Ikeja cewa ya sha bakar azaba a hannun Abba Kyari da yaran sa.

Har ila yau, ya musanta batun yin garkuwa da dan kasuwa Sylvanus Ahamonu da kuma amsar kudin fansa $420,000 daga wurin iyalansa, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Dan KASTLEA ya kashe direban mota da duka a Kaduna

An samu bayanai akan yadda ake zargin Evans tare da wani tsohon soja, Victor Aduba da laifuka hudu, cikin akwai garkuwa da mutane da mallakar da makamai ba bisa ka’ida ba.

Evans ya yi fallasa mai ban mamaki game da Abba Kyari da yaransa
Evans ya ce ya sha bakar wahala a hannun Abba Kyari da yaransa. Hoto: Rundunar Yan Sandan Najeriya.
Asali: Facebook

Ya musanta wannan laifin ne a ranar Juma’a yayin da mai gabatar da kara, Mr Yusuf Sale yake tuhumar sa a kotu.

Evans ya sanar da kotu cewa an haife shi a ranar 22 ga watan Afirilun 1980 kuma shi dan asalin garin Nnewi ne da ke Anambra.

Ya musanta sanin Ahamonu in banda lokacin da ka kama shi bayan ya yi bayani dalla-dalla a cikin bidiyon da aka gabatar wa kotu yana nishadi inda yace ‘yan sanda ne suka takura masa ne akan ya amsa laifin.

A cewar Evans:

Kara karanta wannan

Muna siyo wa masu garkuwa abinci su biya mu N10,000, 'Yan acaɓa da aka kama

“Yan sanda ne suka matsa min akan in yi bidiyon ina murmushi. Baku san irin bakar wahalar da nasha ba a hannun Kyari da yaransa. Na ga bala’i.”
“Duk abinda ku ka ga ina yi su ne suka takura min akan sai na yi hakan.”

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

A wani rahoton, Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alawadai akan kona gonarsa da wasu batagari suka yi a garin Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Kudu a Jihar Binuwai a kwanakin karshen makon nan, The Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar mai shekaru 84 ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan abu kuma ya ce sai jami’an tsaro sun gano wadanda suka tafka ta’asar.

The Punch ta ruwaito yadda batagari suka babbake gonar Orchard wacce mallakin babban mutumin ne na Hilltop da ke Abeokuta a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Annabin 'yan Twitter: Wani ya yi da'awar shi Annabin Allah ne, ya shiga hannun hukuma

Asali: Legit.ng

Online view pixel