Muna siyo wa masu garkuwa abinci su biya mu N10,000, 'Yan acaɓa da aka kama

Muna siyo wa masu garkuwa abinci su biya mu N10,000, 'Yan acaɓa da aka kama

  • Yan sanda a Jihar Oyo sun yi nasarar kama wasu gungun yan acaba da ke siyo wa masu garkuwa da mutane abinci da abin sha
  • Daya daga cikin 'yan acaban da ya shiga hannu, ya bayyana cewa ana biyansu N10,000 a duk lokacin da suka tafi sakon na masu garkuwar
  • Kwamishinan yan sanda na Jihar Oyo, Ngozi Onadeko, yayin holen wadanda ake zargin ta ce rundunar ta samu nasarori sosai saboda tattara bayanan sirri

Ibadan - Wasu gungun mutane sun amsa cewa suna da hannu cikin sace mutane da aka yi a baya-bayan nan a babban titin Legas zuwa Ibadan wacce ta yi sanadin mutuwar wani mutum mai shekara 45, Oluwatosin Anwajoye.

Vanguard ta rahoto cewa wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa suna da hannu a satar mutane da aka yi a ranar 7 ga watan Janairun 2022 a Onigara, babban titin Legas zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Mun gano masu daukar nauyin yan ta'addan Boko Haram guda 96, Lai

An kama 'yan acaɓa da ke siyo wa masu garkuwa da mutane abinci da ababen sha
An kama 'yan acaɓa da ke siyo wa masu garkuwa abinci su biya su N10,000. Hoto: Vangaurd
Asali: Twitter

Shugaban masu acaba, Bashiru Abubakar ne ya bayyana hakan a hedkwatan rundunar yan sanda ta Oyo a Ibadan yayin da kwamishinan yan sanda, Ngozi Onadeko ke yin holensu.

Abubakar ya ce suna yi wa masu garkuwar ayyuka daban-daban da suka hada da siyo musu abinci, ababen sha, ya kara da cewa ana biyansu N10,000 a duk lokacin da suka tafi musu sako, rahoton Vanguard.

Sauran sun hada da Babuga Umaru, Mohammed Umar, Tambaya Usman Shehu, Aliyu Umaru da Isiaka Ibrahim.

Yayin da ta ke jawabi, Kwamishinan ta ce an kama wasu gungun masu garkuwar a babban titin Ijebu-ode-Ibadan da wasu gungun masu fashi da makami a Ibadan.

Ta ce rundunar ta samu nasarori da dama ta hanyar tattara bayanan sirri kuma wadanda aka yi garkuwar da su suna hanyar zuwa domin su tabbatar da wadanda suka yi garkuwar da su.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban ASUU na Jami'ar Gusau, sun sace 'yan uwansa 5 da makwabcinsa

A wani labarin, 'yan bindiga sun kai hari gidan shugaban kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ta Jami'ar Tarayya da ke Gusau, FUGUS, Mr Abdurrahman Adamu, Channels Television ta ruwaito.

A cewar bayanai da aka tattaro, an sace mutane shida yayin harin da aka kai a gidan shugaban ASUUn da ke Damba Quaters, a wajen Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Wani ma'aikacin jami'ar kuma dan uwan shugaban na ASUU ya shaida wa Channels Television cewa yan bindigan sun afka gidan Adamu ne a safiyar ranar Laraba sannan suka sace mutane biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel