Uwa daya uba daya: Yadda mata ta auri dan uwanta na jini, suka haifi 'ya'ya 3 cikin rashin sani

Uwa daya uba daya: Yadda mata ta auri dan uwanta na jini, suka haifi 'ya'ya 3 cikin rashin sani

  • Mukandamage Domitila ta auri dan uwanta na jini ba tare da ta san cewa suna da alaka ba, kuma har sun haifi yara uku tare, ta ce sun gano hakan ne ta wajen yan uwa
  • Domitila ta ce tsawon shekaru biyar kenan rabonta da ji daga dan uwan nata, wanda baya so wani abu ya hada shi da yaransu
  • Mahaifiyar yara ukun tana zaune ne a cikin wani ginin laka da ba a kammala ba kuma uban yaran nata baya taimaka mata

Wata mutumiyar kasar Rwanda, Mukandamage Domitila, ta sanya mutane da dama cikin kaduwa bayan ta bayyana cewa ta auri dan uwanta na jini.

An haifi Domitila a shekarar 1978, amma sai mahafiyarta ta rasu bayan shekara daya. Yan shekaru bayan nan, sai ta sake rasa mahaifinta, kuma tunda tana da yan uwa da yawa, sai suka tashi a gidaje daban-daban.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

Uwa daya uba daya: Yadda mata ta auri dan uwanta na jini, suka haifi 'ya'ya 3 cikin rashin sani
Uwa daya uba daya: Yadda mata ta auri dan uwanta na jini, suka haifi 'ya'ya 3 cikin rashin sani Hoto: AfriMax.
Asali: UGC

Bata ma san yayan nata ba koda dai yan uwa na fada mata cewa tana da wani dan’uwa.

Bayan shekaru masu yawa, sai Domitila ta fara aiki a matsayin mai aikin gida, kuma sai da wata rana ta hadu da dan uwanta a Kigali, Rwanda, koda dai ba su san cewa akwai alaka ta jinni a tsakaninsu ba.

Aure ya kullu

Yan uwan junan sun fada soyayyar junansu sannan Allah ya albarkace su da yara uku. Daga baya, sai suka gano cewa suna da nasaba; uwarsu daya kuma ubansu daya. Wannan ya shafi harkokin Domitila, inda take boyewa a gidanta don gudun haduwa da mutane.

“Na shiga rudani sannan na fara gujewa mutane. Har ta kai na daina diban ruwa…”cewarta a wata hira da AfriMax.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon sanatan Najeriya ya yi babban rashi na mahaifiyarsa

Domitila ta ce mutane kan hantari yaranta sannan su tunatar da su cewa daga tsatso daya suka fito, don haka ta yanke shawarar barin dan uwan nata.

Mahaifiyar yara ukun tana zaune ne a cikin wani ginin laka da ba a kammala ba kuma uban yaran nata baya taimaka mata.

Yaran Domitila na farko da na biyu sana fama da cututtuka daban-daban.

Ta ce tsawon shekaru biyar kenan ba ta ji daga wajen dan uwan nata ba, wanda baya so abu ya hada shi da yaransu.

Domitila ta roki masu fatan alkhairi da su taimaka su gina mata sabon gida sannan su kai yaranta makaranta.

Angon karni: Uwargidar MC tagwaye ta sauka, an samu diya mace

A wani labarin, mun ji cewa Shahararren dan wasan nan na Najeriya, MC Tagwaye, ya zama angon karni bayan Allah ya azurta shi da samun diya mace tare da kyakkyawar matarsa.

Kara karanta wannan

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Ɗaya, Ya Siya Mota Da Babur

Matashin wanda ya yi suna saboda wasan barkwanci da sunan shugaba Muhammadu Buhari, ya sanar da labarin samun karuwan a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya kuma wallafa hoton kyakkyawar yarinyar.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin nasa, an gano wasu daga cikin yan uwa da abokan arziki da suka zo domin yiwa ma'auratan san barka da samun kyautar Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel