Angon karni: Uwargidar MC tagwaye ta sauka, an samu diya mace

Angon karni: Uwargidar MC tagwaye ta sauka, an samu diya mace

  • Allah ya azurta shahararren me wasan nan na barkwanci, MC tagwaye da samun karuwan diya mace
  • Matashin da kan yi wasan barkwanci da sunan shugaba Buhari, ya je shafinsa na soshiyal midiya domin sanar da kyautar da Allah ya yi masa tare da wallafa hoton jaririyar
  • Ya kuma bayyana sunan yarinyar a matsayin Maryam Iruoma Nadia

Shahararren dan wasan nan na Najeriya, MC Tagwaye, ya zama angon karni bayan Allah ya azurta shi da samun diya mace tare da kyakkyawar matarsa.

Matashin wanda ya yi suna saboda wasan barkwanci da sunan shugaba Muhammadu Buhari, ya sanar da labarin samun karuwan a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya kuma wallafa hoton kyakkyawar yarinyar.

Angon karni: Uwargidar MC tagwaye ta sauka, an samu diya mace
Angon karni: Uwargidar MC tagwaye ta sauka, an samu diya mace Hoto: @mc_tagwaye
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin nasa, an gano wasu daga cikin yan uwa da abokan arziki da suka zo domin yiwa ma'auratan san barka da samun kyautar Allah.

Kara karanta wannan

Tinubu ne zai ci: Malamin addini ya yi hasashen zaben 2023

Ya kuma bayyana suna jinjirar a matsayin Maryam Iruoma Nadia.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya wallafa a shafin nasa:

"Kunshin farin cikinmu, gimbiyata...Maryam Iruoma Nadia."

Tuni masoya suka dunga aike masa da sakon taya murna.

rukkayahsdiary ta rubuta:

"Ta hadu sosai MashaAllah TabarakaAllah Allah ya raya mana it’s Amin."

gimbiya_shatou ta ce:

"Ya salam❤️❤️❤️hoto na biyu✌❤️❤️❤️❤️MashaAllah"

saratityn_baba ta rubuta:

"Maa shaa Allah sabon uba "

asabsey ta ce:

"Ina taya ka murna. Allah ya raya ta."

MC Tagwaye; mai barkwanci ta hanyar kwaikwayon Buhari ya auri diyar hadimar shugaban kasa

A baya mun kawo cewa mai wasan barkwanci, Obinna Simon, wanda aka fi sani da 'MC Tagwaye', ya angonce da amaryarsa Hauwa, diyar Maryam Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin jin dadin 'yan kasa.

Da safiyar ranar Lahadi ne Maryam Uwais, uwar amarya, da kanta ta yada hotunan bikin MC Tagwaye da Hauwa a shafinta dandalin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

Ta ce:

"A yau ne diyata, Hauwa, ta yi aure. Na yi sabon da, MC Tagwaye. Za su kasance cikin soyayya, raha da barkwanci duk inda suka samu kansu, daga nan har zuwa karshen rayuwarsu.
"Ina neman ku taya wadannan sabbin ma'aurata murna da addu'a. Aure ba abu ne mai sauki ba. Amma addu'arku da taimakon Ubangiji zai taimakesu a cikin rayuwarsu ta aure."

Asali: Legit.ng

Online view pixel