Tashin hankali: Masu garkuwa da mutane sun 'kwace' iyakokin jihohi 2 a Najeriya

Tashin hankali: Masu garkuwa da mutane sun 'kwace' iyakokin jihohi 2 a Najeriya

  • Miyagun 'yan ta'adda sun kwace iyakokin jihar Abia da na Imo inda suke cin karensu babu babbaka
  • Mazauna yankin suna koka wa kan halin da suka shiga inda miyagun ke sace mutane ko su kashe su a kowacce rana
  • Dalibai sun ce hakan babban kalubale ne ga karatun su yayin da mazauna yankin ke korafi kan halin ko in kula da gwamnati ta nuna musu

Masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga sun kwace titin da ke tsakanin Uturu na karamar hukumar Isiukwiato da ke jihar Abia zuwa karamar hukumar Okigwe na jihar Imo.

A binciken da Daily Trust tayi, ya bayyana yadda yan ta'addan suke cin karen su ba babbaka kan titin, a kowacce rana ko dai su kashe ko kuma su yi garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Jihar Neja: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe sojoji 3 da mazauna da yawa

Tashin hankali: Masu garkuwa da mutane sun 'kwace' iyakokin jihohi 2 a Najeriya
Tashin hankali: Masu garkuwa da mutane sun 'kwace' iyakokin jihohi 2 a Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tsakanin Disamba zuwa Janairu, an yi garkuwa da kimanin mutane 25, inda aka halaka mutane biyar, duk da akwai matsayar jami'an tsaro guda biyu a kan titin.

Mazauna yankin Uturu sun nuna damuwar su matuka game da yadda ake kashe-kashe da garkuwa da mutane a kan titin Okigwe zuwa Uturu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban Shugaban yankin Uturu, Chief Chidi Uturu Ogbaegbe, wanda ya zanta da Daily Trust, yace shugaban yan ta'addan ya yi amfani da lalacewar titin a matsayin damar tsaida mutane kan titin Ihube zuwa Okigwe.

Ya ce, "Al'amarin da ke aukuwa kan titin dake tsakanin Imo zuwa jihar Abia, musamman hanyar zuwa Jami'ar jihar Abia, ya na daya daga cikin abubuwan da suke tada hankulan mu."
"Mutane sun kusa daina bin hanyar saboda ayyukan masu garkuwa da mutane da yan bindiga. Dalibai da mutanen anguwa basa iya tafiya jihar Imo cikin kwanciyar hankali. Maganar gaskiya, duk wanda za su bi hanyar su na bi ne a tsorace saboda basu da tabbacin dawowa da ransu."

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Ogbaegbe ya nuna matukar rashin jin dadinsa a kan yadda hakan ke aukuwa duk da akwai matsayar jami'an tsaro da dama a kan titin.

Ya yi kira ga hukumar kula da tituna da su tabbatar da tsaro a kan hanyar ga matafiya.

Haka zalika, yayin tattaunawa da Daily Trust a kan yana bukatar a sakaya sunansa, wani dalibin Uturu na jami'ar jihar Abia, wanda ya ke zaune Okigwe, a Imo, ya ce a halin yanzu barazana ce ga karatu a jamiar.

"Damuwa ta a yanzu shi ne yadda gwamnatin jihar Abia da Imo ba su nuna damuwarsu a kan rashin tsaron ba. Ba mu iya zuwa makaranta saboda hakan barazana ce ga rayuwa. Ina kira ga gwamnatin jihohi biyun da su shiga cikin al'amarin domin su ceto jama'a daga mummunan al'amarin," a cewarsa.

Asari Dokubo ya kira Nnamdi Kanu da IPOB da sakarkaru, ya ce babu yadda za su yi da shi

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige yayan kwamishina a jihar Benue

A wani labari na daban, shugaban tsagerun yankin Niger Delta, Mujahid Asari Dokubo ya sake suka tare da caccakar 'yan awaren IPOB da shugabansu, Mazi Nnamdi Kanu.

The Nation ta ruwaito cewa, Dokubo ya soki 'yan awaren kuma ya yi musu wankin babban bargo kan cewa da suka yi ya na da hannu wurin dawo da Kanu kasar Najeriya daga Kenya.

The Nation ta ruwaito cewa, Kanu da Dokubo ba su ga maciji kan batun kafa kasar Biafra, dalilin kuma da ya hada su a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel