Kaduna: An kashe mutane 5, an ƙona gidaje da dama a sabon harin da 'yan bindiga suka kai a Atisa

Kaduna: An kashe mutane 5, an ƙona gidaje da dama a sabon harin da 'yan bindiga suka kai a Atisa

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sake kai hari garin Atisa da ke karkashin karamar hukumar Zangon Kataf a Kaduna
  • Wannan harin na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan wasu maharan sun kai farmaki a garin Kurmin Masara inda suka halaka a kalla mutane 11
  • Gabriel Joseph, Shugaban Matasan Masarautar Atyap, ya ankarar da hukuma cewa maharan suna son yi musu kisan kare dangi ne don haka ya yi kira ga gwamnati da dauki mataki

Kaduna - Ƙasa da awa 24 bayan kashe mutane 11 a Kurmin Masara a masarautar Atyap, Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Jihar Kaduna, yan bindiga sun sake kai hari Kurmin Masara sun kashe mutane 5 a daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

Wata majiya daga kauyen da ke makwabtaka ya shaida wa Channels Television cewa maharan sun isa garin ne misalin karfe 9.50 na dare suka shafe kimanin awa ɗaya suna cin karensu ba babbaka, rahoton Daily Trust.

Kaduna: An kashe mutane 5, an ƙona gidaje da dama a sabon harin da 'yan bindiga suka kai a Atisa
An kashe mutane 5, an kona gidaje a sabon harin Zangon Kataf. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ya ce:

"Saboda yawancin mutanen Kurmin Masara sun tsere daga gidajensu, maharan sun kai harin ne a Atisa, wani gari da ke kusa da Kurmin Masara."

Suna son ganin bayan mu ne, Gabriel Joseph

Shugaban Matasan Masarautar Atyap, Gabriel Joseph, ya janyo hankalin al'umma cewa maharan suna son yi musu kisan kare dangi ne.

Ya yi kira ga gwamnati ta dauki ƙwararan matakai don ganin ta kare mutanen yankin tare da tsare musu kayayyakin su.

Shugaban karamar hukumar Zangon Kataf ya tabbatar da harin

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Francis Sani, shugaban ƙaramar hukumar Zangon Kataf, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta binciko wadanda suka kai harin.

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.

Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel