'Yan sanda sun koma soja bisa aikata 'fashi da makami' a Yobe

'Yan sanda sun koma soja bisa aikata 'fashi da makami' a Yobe

  • 'Yan sanda a Jihar Yobe sun yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi da balle gida tare da fashi da makami
  • Wadanda ake zargin, cikinsu har da jami'in soja sun kutsa gidan wata Hajiya Aisha Usman ne suka mata fashin kudi, mota da waya salularta
  • Rahoton afkuwar lamarin ya nuna cewa wadanda ake zargin sun raunata matar da dan ta mai shekaru 17 yayin da suka yi kokarin daure su da wayar wuta

Jihar Yobe - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu mutane uku da ta zargi da hadin baki, balle gida da fashi da makami cikinsu har da jami'in soja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wadanda ake zargin sun ktsa gidan wata Hajiya Aisha Usman mazauniyar Sabon-Pegi na da tsakar dare.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

'Yan sanda sun koma soja bisa aikata 'fashi da makami' a Yobe
An kama soja saboda aikata fashi da makami a Yobe. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Dauke da muggan makamai, ciki har da AK-47, wadanda ake zargin sun kwashe wa matar kudi N250,000, motar kirar Peugeot 307 Saloon da wayar salula kirar Nokia, rahoton Daily Trust.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, Mai Magana da Yawun Yan sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ya ce wadanda ake zargin sun yi wa wacce abin da ya faru da ita munanan rauni tare da dan ta Ahmed Umar mai shekaru 17 bayan kokarin daure su da wayar satelite.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164