Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

  • Sakamakon neman wata da mijinta ke yi, wata mata ta aika Uban 'yayanta barzahu ta hanyar gogeshi da dutsen guga
  • Wannan mumunan abu ya auku ne a unguwar Abule-Egba dake jihar Legas, Kudu maso yammacin Najeriya
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma an damketa

Legas - Wata matar aure, Motunrayo, ta hallaka mijinta mai suna Alaba Bama a unguwar Abule-Egba ta jihar Legas bayan mujadalar da ta auku tsakaninsu.

Punch ta ruwaito cewa Motunrayo ta dannawa mijinta dutsen guga a kirjinsa kuma sakamakon haka ya mutu.

Mijin wanda shi ne mammalakin gidan saukan bakin, Bama Hotel, ya mutu ne ranar Litinin, 14 ga Junairu, 2022.

Uwargida ta kashe miji
Uwargida ta dannawa mijinta dutsen gudu har lahira don yi dirkawa wata ciki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu

Me ya faru tsakaninsu?

An samu ruwayoyi biyu game da abinda ya haddasa rikici tsakanin ma'auratan.

Wani mutumi mai suna, Kelly Hassino, ya ce Motunrayo ta gano mijin ya yiwa wata mata ciki.

A jawabin da ya saurara a shafin Facebook, yace:

"Matar mai gidan Otel na Bama dake Abule Egba a jihar Legas ta kashe shi daren jiya yayinda yake bacci bayan ta gano ya yiwa wata juna biyu."
"Mutumin wanda ya shahara da suna 'Bama' kwanan nan ya dawo daga Dubai tare da yaransu uku bayan hutun da suka je. Shekarunsu 8 tare."
"Sai da ta bashi kwaya, yayi bacci, sannan ta danna masa dutsen guga mai zafi a sassan jikinsa sai da ya mutu."

Wata majiyar daban kuma tace rikici ya barke ne tsakaninu saboda mijin ya ki korar wata mai aiki da matar ta bukata a kora.

Majiyar tace Motunrayo ta bayyana cewa da suka fara fada, ta yi amfani da dutsen guga mai zafi wajen konashi a kirji.

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Kaakin hukumar yan sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da lamarin kuma yace tuni an damke matar da wasu mutum uku dake da hannu cikin laifin.

Yace:

"An ajiye gawarsa a asibitin Yaba don bincike. An damke matar mamacin tare da wasu mutum uku."

An gurfanar da Saurayi gaban kotu kan yaƙi ɗaukar nauyin cikin da ya ɗirkawa budurwarsa

A wani labarin kuwa, Kotun Majirtire ta garƙame matashi ɗan shekara 24, Korode Yusuf, bisa ƙin ɗaukar ɗawainiyar cikin da ya ɗirkawa budurwarsa a jihar Ogun.

Premium Times ta rahoto cewa Yusuf, wanda ke zaune a No. 6 layin Kajola Oluwa, dake yankin Isale Ariya, na fuskantar tuhuma ne kan zargin jefa rayuwar wani cikin hatsari.

Mai gabatar da ƙara, E. O. Adaraloye, ya shaida wa kotu cewa, wanda ake ƙara ya aikata wannan ɗanyen aiki ne a ranar 1 ga watan Maris, 2021, a ɗakinsa da yake zaune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel